Kano 9: An mika yaran da aka sace zuwa Anambara ga gwamnatin Kano

Kano 9: An mika yaran da aka sace zuwa Anambara ga gwamnatin Kano

Hukumar yan sandan Najeriya ta mika yara takwas cikin tara da aka sace daga jihar Kano kuma aka sayar dasu a jihar Anambara ga gwamnatin jihar Kano.

An bayyana cewa na taran na fama da rashin lafiya kuma ana jinyarsa a asibiti a babbar birinin jihar.

Gwamnan jihar Kano wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Ajhaji Usman Alhai, ya siffanta gano wadannan yara a matsayin ikon Allah kuma yan sanda sun nuna kwarewarsu wajen yaki da ta'addanci.

Yace; "Ina yabawa kwamishanan yan sanda da sashen yaki da satar mutane kan ceto yaran nan. Tun lokacin da abun ya faru, hukumar yan sanda ta tabbatar da ba'a samu matsala ba."

Kwamandan sashen yaki da satar mutane shiyar jihar Kano, CSP Babagana Saje, yayinda yake mika yaran ya bayyana cewa garkuwa da yaro daya ya sa hukumar damke masu laifin, har aka gano ashe akwai wadanda suka kware wajen satan yara daga Kano zuwa Onitsha.

SHIN KA SAN An sake bankado gidajen ladabtar da fandararru 2 marasa rijista a jihar Kaduna

Yace: "Mun damke wasu, wani mutum da matarsa, wadanda suke satan yara a nan zu sayar a Onitsha."

Suna sayar da yaran N200,000 ga wata mata a Onitsha. Ita kuma ta sayar da yaran ga kwastomominta a a Legas. An samu biyu daga cikin yaran a wajen a matsayin masu aikin gida."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel