Idan da ranka ka sha kallo: Mamaci ya nemi a budeshi daga kabarinsa ya dawo duniya

Idan da ranka ka sha kallo: Mamaci ya nemi a budeshi daga kabarinsa ya dawo duniya

Wani lamari mai kama da almara ya faru a kasar Ireland wanda ya daure ma mutane da dama kai, suka gaza fahimtarsa har sai daga baya, wannan lamari kuwa shine yadda wani mamaci ya yi magana bayan an turbudeshi a cikin kabarinsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani mutumi mai suna Shay Bradley ya rasu, inda yan uwa da abokan arziki suka garzaya zuwa makabarta domin a binneshi a gabansu, sai dai jim kadan bayan rufeshi sai suka ji shi yana magana.

KU KARANTA: Yaki da Boko Haram: Buhari zai sayo sabbin jiragen yaki daga kasar Rasha

“Ku budeni na fito, duhu ya yi yawa a nan.” Wannan shine abinda aka jiyo Shay yana fadi, wanda hakan ya tsorata masu jimamin mutuwar tasa har wasu suka yi kokarin tserewa, amma dai duka suka taru suka yi ta maza suka tsaya don sanin daga inda maganar ke fitowa.

Mamacin ya cigaba da cewa: “Ina ne nan? Shin muryar Fasto nake ji? Ni ne Shay, kuma ni ne a cikin wannan akwatin gawar.” Daga nan kuma sia ya fara waka “Kuna ji na? kuna ji na? ni ne, na kira ne kawai don yi muku bankwana.”

Sai bayan wannan maganan karshe ne mahalarta jana’izar suka fahimci ashe tun kafin ya rasu ya nadi wannan maganar, kuma ya ajiyeta a cikin ramin da ya zaba a turbudeshi a ciki, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Wannan lamari ya faru ne a ranar 12 ga watan Oktoba a makabartar arna dake Kilmanagh Kilkenny na kasar Ireland inda aka binne Shay, wanda tsohon hafsan Sojan kasar ne, hakan ya sanya mahalarta jana’izar murmushi a maimakon kuka.

Sai dai diyarsa mai suna Andrea ta bayyana cewa mahaifinta ya kwashe shekaru uku yana jinya, amma duk da haka sai ya nemi yaronsa Jonathan ya shirya masa wani abu da zai kayatar da mutane bayan mutuwarsa, don haka suka tsara wannan barkwancin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel