Bayan shekaru aru-aru, an fara hada fensir a Najeriya

Bayan shekaru aru-aru, an fara hada fensir a Najeriya

Wani kamfani ya kaddamar da hada fensira a Najeriya ta hanyar amfani da tsaffin jaridu.

Ministan Kimiya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce kamfanin na da ikon hada fensira dozin milyan 2.4 a shekara.

A ranar Litinin a Abuja, ya karbi bakuncin kamfanin hada fensiran mai suna Bamib Resources & Investments Company Ltd, inda yace:

"Muna yaba muku kan aikin da kuka yi domin jin dadin kasarmu. Lokacin da na ziyarci wata ma'aikatarmu a Enugu, na ga cewa sun bincike kan yadda ake hada fensira. Abin ya bani takaici da suka fada min cewa babu kamfanin hada fensira a Najeriya."

"Sun ce an taba yi kamfanonin a baya amma duk a kullesu, abin ya dameni."

"A matsayin ministan Kimiya da Fasaha, na yi nazarin cewa fensir da yara da manya ke amfani da shi kuma da sauki, ya kamata kasa irin Najeriya ta rika hada dukkan fensiran da ake bukata. Sai na tabbatar da cewa ma'aikatar ta Enugu ta cigaba da bincikenta."

"Ba wai ina son mu fara hada fensira da kawai ace muna yi bane amma ace dukkan kayan hadawan muna da su a Najeriya kuma zai taimaka wajen samar da aikinyi, samar da arziki, kawar da talauci."

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dira birnin Sochi, kasar Rasha (Hotuna)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel