Jihar Yobe za ta fara amfani da harshen Hausa wurin koyarwa a makarantun frimare

Jihar Yobe za ta fara amfani da harshen Hausa wurin koyarwa a makarantun frimare

Hukumar Ilimin Frimari na jihar Yobe (SUBEB) ta ce jihar za ta fari amfani da harshen Hausa a matsayin yaren da za a rika amfani da shi wurin koyar da yara a makarantun frimari kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban SUBEB na jihar Yobe, Goni Ibrahim ne ya sanar da manema labarai hakan a Bauchi yayin taron horaswa da hukumar ta shirya wa malaman jihar tare da hadin gwiwar Bankin Duniya da Northern Education Initiatice (NEI Plus).

Ibrahim wanda ya samu wakilcin Direktan Hada kan al'umma na hukumar, Sama'ila Machina ya ce an cimma matsayar fara amfani da harshen hausa wurin koyarwa a makarantun ne domin inganta koyarwa da fahimtar karatu.

DUBA WANNAN: Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

Ya yi bayanin cewa sabon tsarin na amfani da harshen hausa zai saukaka wa yara fahimtar karatu musamman daga aji 1 zuwa 3 na frimare inda ya kara da cewa shirin zai taimaka wurin kawar da jahilci a jihar.

A bangarensa, jami'in shirin inganta ilimi na jihar Yobe (BESDA), Samaila Machina ya bayyana cewa amfani da harshen iyayen wurin koyarwa da aka yi wa lakabi da 'Early Grade Reading' zai fara aiki ne kan dalibai 81,116 na makarantun frimare a zangon karatu na 2019/2020 a jihar.

Ya yi bayyanin cewa BESDA shiri ne da ya samu tallafi daga Bankin Duniya domin taimakawa yara da ba su zuwa makaranta kamar Almajirai da yara mota domin su samu ilimi a johohin arewa 17 ciki har da jihar Yobe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel