Shugaba Buhari ya dira birnin Sochi, kasar Rasha (Hotuna)

Shugaba Buhari ya dira birnin Sochi, kasar Rasha (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira babban filin jirgin saman Sochi, kasar Rasha domin halartan taron kwana 3 na hadin gwiwar Rasha da nahiyar Afrika, inda za'a tattauna kan zaman lafiya, tabbatar da tsaro da cigaba.

Jirgin shugaban kasan ya dira filin jirgin saman ne misalin karfe 11:25 na dareLitinin kuma ya samu kyakkyawan tarba daga magajin garin Sochi, Anatiliy Nikolayevich Pakhomov, da wasu manyan jami'an gwamnatin jihar.

Za'a yi taron tattauna tattalin arziki a ranar 23 da 24 ga watan Oktoba, 2019, kuma za'ayi zama hudu. Akalla shugabannin kasashen Afrika talatin ne zasu halarci taron.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana a jawabin da ya saki a daren Litinin.

Ya ce a yanzu, akwai tarurrukan hadin gwiwa da Afrika na Amurka, Indiya, Sin da Japan, kuma Najeriya ta amfana da dukkansu.

Shugaba Buhari ya tafi da gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, Bello Matawalle na jihar Zamfara da Kayode Fayemi na jihar Ekiti.

Hakazalika, akwai ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama; ministan hannun jari, Adeniyi Adebayi; ministan ma'adinai, Olamilekan Adegbite da ministan man fetur, Temipre Sylva.

Hotunan:

Shugaba Buhari ya dira birnin Sochi, kasar Rasha (Hotuna)
Shugaba Buhari ya dira birnin Sochi, kasar Rasha (Hotuna)
Asali: UGC

Shugaba Buhari ya dira birnin Sochi, kasar Rasha (Hotuna)
Shugaba Buhari ya dira birnin Sochi, kasar Rasha (Hotuna)
Asali: UGC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel