Tawagar hazikin dan sanda Abba Kyari sun kama masu garkuwa da mutane 81

Tawagar hazikin dan sanda Abba Kyari sun kama masu garkuwa da mutane 81

Rundunar yan sandan Najeriya a jiya Litinin, 21 ga watan Oktoba, a Abuja ta gurfanar da masu garkuwa da mutane 81 wadanda aka kama a jihohin Kaduna da Taraba da sauran sassa na kasar.

Yayin da ake gurfanar da masu laifin, kakakin rundunar Frank Mba, yace daga cikinsu akwai kungiyar yan Chadi da Nijar wadanda suka shahara a wajen sace mutane, da kuma tsoffin yan fursuna shida wadanda suka sace wani dan kasuwa kuma dan majalisa a Sokoto.

An tattaro cewa tawagar hazikin dan sanda DCP Abba Kyari ne suka yi nasarar kama su.

Haka zalika an kama kungiyar yan fashi masu amfani da kayan soji da na rundunar sojin saman Najeriya wadanda masu garkuwa da mutane a Sokoto suka kafa a yayin da suke gidan yari a Katsina. Wadannan mutane sun hada da Rufai Muhammed, Isah Abdullahi, Abdulrasheed Labaran, Abba Zayyanu, Ayuba Awwalu, da Rabiu Ibrahim.

Shugaban kungiyar mai suna Mohammed wanda yayi magana yace “mun zama abokai ne a lokacin da muka zauna a gidan yarin Katsina."

Yace kungiyar tayi fashi a hanyar Zaria/Kaduna/Kano sau 12 sun kuma karbi miliyoyin nairori a matsayin kudaden fansa daga hannun mutanen da suka sace.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta rufe cocin Anambra saboda yawan hayaniya

Sai kuma 'yan dafara ta yanar gizo guda goma, harda 'dan kasar Ghana a cikinsu.

Ansami bindigogi kirar AK47 guda takwas da harsashi guda 347, da wasu manyan makamai guda 15, Computer guda 10, da zunzurutun kudi naira million 10 wanda suke karba kudin fansa a hannun wadanda suke kamawa.

Ga hotunan a kasa:

Tawagar hazikin dan sanda Abba Kyari sun kama masu garkuwa da mutane 81
Tawagar hazikin dan sanda Abba Kyari sun kama masu garkuwa da mutane 81
Asali: Facebook

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel