Jiki magayi: Kotu ta sassauta ma Sowore tsauraran sharadin belin da ta gindaya masa

Jiki magayi: Kotu ta sassauta ma Sowore tsauraran sharadin belin da ta gindaya masa

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Abuja ta sassauta sharuddan belin da ta gindaya ma shugaban kawo juyin juya hali a Najeriya, kuma mawallacin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito baya ga Sowore, kotun ta sassauta ma abokinsa da ake tuhumarsa tare, Olawale Bakare, inda dukkaninsu ana tuhumarsu da aikata laifin cin amnar kasa ne.

KU KARANTA: Ku rage farashin sayen Data – Minista Pantami ga kamfanonin sadarwa

Alkalin kotun, Ijeoma Ojukwu ce ta yanke wannan hukunci a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba inda tace ta rage masa kudin beli naira miliyan 100 da ta sanya masa zuwa naira miliyan 50, sa’annan ta rage sharadin beli na naira miliyan 50 ga Bakare zuwa naira miliyan 20.

Haka zalika majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkali Ojukwu ta sassauta sharadin cewa lallai sai masu tsaya ma mutanen biyu sun ajiye shaidan suna da kwatankwacin wannan kudi a asusunsu da kotu, inda tace ta janye wannan sharadin shima.

Gwamnatin Najeriya na tuhumar Sowore da Bakare ne a kan laifuka guda 7 da suka danganci karkatar da kudade, cin zarafi a yanar gizo, cin amanar kasa da dai sauransu.

Idan za’a tuna, Sowore ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC a zaben shekarar 2019 daya gudana a ranar 23 ga watan Feburairu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng