Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa dan'uwan Sheikh Isa Pantami rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa dan'uwan Sheikh Isa Pantami rasuwa

Inna Lillahi wa inna ilaihi raji'un!!!

Allah ya yiwa babban yayan ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, rasuwa a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, 2019.

Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na ra'ayi da sada zumunta, yace:

"Allah Ya yiwa dan'uwana, Is'haq Ali Ibrahim, rasuwa yau. Allah ya gafarta masa, ya masa rahama."

Daga Legit.ng, muna addu'a Allah jikansa, ya rahamshesa kuma ya tabbatar da shi wajen tambaya. Amin.

A bangare guda, Ministan sadarwa na Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya umarci dukkanin kamfanonin sadarwa dake Najeriya dasu rage farashin sayen Data da ake amfani dashi wajen shiga shafukan yanar gizo, in ji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Pantami ya umarci hukumar sadarwa ta Najeriya, NCC ta dabbaka wannan umarni nasa a kan kamfanonin sadarwa ne, sa’annan ya umarci NCC ta dakatar da yadda kamfanonin suke zaftare ma abokan huldansu Data.

KARANTA: Gobara ta kama a matatar man fetur mafi girma a kasar Iran

Hadimin ministan a kan kafafen sadarwa na zamani, Yusuf Abubakar ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda yace ministan ya bada wannan umarni ne bayan NCC ta mika masa rahoton ayyukan da suka a gaba da kuma muradunsu na karamin zango.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel