Yanzu-yanzu: An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Kogi

Yanzu-yanzu: An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Kogi

An rantsar da Mista Edward Onoja a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kogi a ranar Litinin, 21 ga Oktoba a gidan gwamnatin Lugard House dake Lokoja, babbar birnin jihar.

An rantsar da Onoja bayan ya bayyana gana majalisar dokokin jihar da safe kuma suka tantanceshi kafin tabbatar da shi.

Alkalin alkalan jihar, Nasir Ajana, ya rantsar da shi.

Daga cikin wadanda suke hallare a taron sune gwamna Yahaya Bello, mambobin majalisar da manyan jami'an gwamnati.

Yanzu-yanzu: An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Kogi
sabon mataimakin gwamnan jihar Kogi
Asali: Facebook

KU KARANTA: Bayan sa'o'i 40, Zakin gidan Zoo na Kano ya koma keji da kansa (Bidiyo)

Majalisar dokokin jihar Kogi ta fito ta yi karin haske game da tsige mataimakin gwamna Simon Achuba da tayi. Majalisar jihar tace tuni dai bakin alkalami ya riga ya bushe. Jaridar Vanguard.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Kogi, Honarabul Moses Akande ya zargi kwamitin da aka kafa na musamman domin ya binciki tsohon mataimakin gwamnan jihar da yin ba daidai ba a aikinsu.

‘Dan majalisar mai wakiltar shiyyar Ogorimangogo a jam’iyyar APC da yake magana a madadin daukacin majalisar dokokin jihar yace ba a sa wannan kwamiti ta fitar da wata matsaya ba, illa ta yi bincike.

Majalisar tace sashe na 188(11) na kundin tsarin mulki ya ba ta wannan dama. Akande yake cewa bai san daga inda rahoton kwamitin yake yawo ba bayan da farko shugaban kwamitin ya kira aikin da sirri.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel