Za mu ba Mawakan Afrika goyon baya wajen biki AAMA – Inji Lai

Za mu ba Mawakan Afrika goyon baya wajen biki AAMA – Inji Lai

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sha alwashin bada cikakken goyon baya wajen daukar nauyin bikin AAMA na Makada da Mawakan Nahiyar Afrika. Za a yi taron bana ne a karshen watan gobe.

Yanzu haka an fara shirin daukar nauyin bikin bana wanda za a yi a Garin Legas. Za a yi bikin raba kyauta ga Mawaka da Makadan da su ka shahara a shekarar nan ne a Watan Nuwamba.

Ministan al’adu da yada labaran Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar Ranar Lahadi, 19 ga Wata a Garin Legas domin bayyana matsayar gwamnatin.

“Idan ku ka duba bikin All Africa Music Awards, ya na cikin manyan taron yabon gwanin Mawaka da ake yi a Afrika a Afrika. Abin da gwamnati ta saba yi shi ne, ta bada wurin yin wannan taro.”

“Mun bada goyon baya ga AFRIMA, mun ba su gudumuwar da su ke bukata, kuma tarihi ya nuna cewa bukuwan AFRIMA da aka shirya a Najeriya su na cikin mafi ban kayen da aka shirya.

KU KARANTA: An fitar da sunayen manyan 'yan kwallon Duniya a karni na 21

“Haka bana a shirye mu ke, mu hada-kai mu yi aiki da AFRIMA, mu ba su duk goyon bayan da ake bukata na daukar hoton da kuma taimaka masu wajen samun goyon masu ruwa da tsaki.”

Alhaji Lai Mohammed ya kuma bayyana cewa Najeriya ta yi nasara wajen daukar nauyin wannan babban taro ne saboda rage tsaurin da aka yi wajen samu takardun shiga kasar cikin sauki.

An yi bikin AFRIMA na farko ne a 2014 inda kungiyar AU ta shirya domin ba wadanda su ka yi fice wajen kawowa al’adun Afrika cigaba. Za a yi bikin bana a Ranar 20 zuwa 23 na Nuwamba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel