Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 57 a Jamhuriyyar Nijar

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 57 a Jamhuriyyar Nijar

A yayin da ake tsananin bukatar agajin jinkai cikin gaggawa, mahukunta a kasar Nijar sun bayyana rahoton yadda ambaliyar ruwa ta tilasta wa mutane dubu 23 tserewa daga muhallansu kamar yadda Muryar Duniya ta wallafa.

Majiyar rahoton ta ruwaito cewa, mamakon ruwan sama da aka rinka shatatawa tamkar da bakin kwarya cikin tsawon watanni uku da shude a baya bayanan, ya yi sanadiyar tumbatsar tekunan Komadougou na Yobe da suka hade da tafkin Chadi, da suka haddasa ambaliyar ruwa daga kananan tafkuna da gulabe a sassa daban-daban na kasar Najeriya da kuma makociyarta.

Alkalumma sun tabbatar da yadda ambaliyar ruwa tayi share wasu kananan kauyuka biyu da ke jihar Diffa a Kudu maso Gabashin Jamhuriyyar Nijar, lamarin da ya tilastawa magidanta 2,500 tsere wa daga muhallansu domin neman mafaka.

Wata kididdiga ta nuna yadda ruwa ya cinye wasu kananun kauyuka biyu da ke jihar Diffa wanda ya tilastawa magidanta dubu 2 da dari 5 ficewa don neman mafaka.

Haka kuma alkalumma sun nuna cewa ya zuwa yanzu akwai iyalai kimanin 400 da ke rayuwar fargaba cikin bukkoki a kauyuka biyu wadanda a koda yaushe ambaliyar ruwa na iya riskarsu.

KARANTA KUMA: Karar Kwana: Zazzafan fate ya salwantar da rayukan kananan yara 3 a Bauchi

Baya ga raba mutane da muhallansu da ambaliyar ruwan ta yi sanadi, ta kuma salwantar da amfanin gona gami da rusa mafi akasarin gidajen kauyukan da ke iyaka da tafkunan.

A tsakanin watan Yuni zuwa Satumban da suka gabata, ambaliyar ruwa ta salwantar da rayukan mutane 57 yayin da kimanin mutane dubu 130 suka rasa matsugunansu a sassa daban-daban na Kudu maso Gabashin kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel