Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

Daya daga cikin daya daga cikin matan da aka ceto daga wani haramtaccen gidan 'azabtarwa' da ke kira gidan malam Niga a Kaduna ta bayyana yadda ake zina da su a gidan.

Wannan na zuwa ne bayan jami'an tsaro a Kaduna sun bankado wani haramtaccen gidan a unguwar Rigasa da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Channels tv ta ruwaito cewa gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai, a ranar Asabar da kansa ya halarci wurin sumamen da jami'an tsaro suka kai a ranar Asabar kusan makonni 3 bayan 'yan sanda sun ceto wasu mutane 300 a wani gida mai kama da wannan a Rigasa.

Kimanin mutane 147 ciki har da mata 22 biyu 'yan kasan waje ne 'yan sandan suka ceto inda suka samu da yawansu daure cikin mari.

Da ta ke bayyana halin da suka shiga a wurin, wata budurwa ta shaidawa Channels Television cewa surukin mai gidan, Malam Niga ya sha zuwa ya yi zina da ita da sauran matan.

Ta jadada cewa sun sha kai kararsa wurin Malam Niga amma bai saurare su ba inda ya ce surukinsa ba zai taba aikata irin wannan abin ba.

A cewar budurwar da aka ceto, diyar mai gidan, Fatima ta san zaluncin da mijinta ya ke yi.

Ta kara da cewa Fatima tana hukunta su ko kuma tayi fada da mijinta duk lokacin da ta lura yana harka da daya daga cikin 'yan matan da ke gidan 'azabtarwar'

DUBA WANNAN: Tirkashi: Ba don doka ba, da na bindige mahaifi na har lahira, inji jarumi Dabo

Ga bidiyon a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel