Jami'ar horar da 'yan sanda ta Wudil ta bayyana ranar fara tantance dalibai

Jami'ar horar da 'yan sanda ta Wudil ta bayyana ranar fara tantance dalibai

- Hukumar 'yan sandan jihar Kaduna ta sanar da ranara fara tantance daliban da sunansu ya fito na jami'ar 'yan sandan Kano dake Wudil

- Za a fara tantancewar ne a ranar 24 ga watan Oktoba, 2019 inda za a duba takardu tare da lafiyar daliban da suka yi nasarar cin jarabawar shiga jami'ar

- Ana kira ga daliban da su tafi da ainihin takardun karatunsu da kuma fotokwafinsu 15 da sauarna abubuwan amfaninsu don tantancewar

Hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna ta sanar da cewa, jami’ar ‘yan sanda da ke Wudil zata fara tantance dalibai karo na bakwai a ranar 24 ga watan oktoba.

Mai magana da yawun jami’ar, DSP Yakubu Sabo ya bayyana hakan a takardar da ya bawa manema labarai a ranar Juma’a a garin Kaduna.

Za a fara tantancewar ne a jami’ar a ranar 24 ga watan Oktoba inda za a fara da dalibai yankin arewa maso yamma.

KU KARANTA: Bita da kulli: Bayan tsige mataimakin gwamnan, jami'an tsaro sun zagaye gidansa

Takardar ta bayyana cewa, daliban da suka samu tsallake jarabawar shiga makarantar da aka rubuta a ranar 24 ga watan Oktoba su garzaya zuwa jami’ar dake Wudil don tantancewa. Ta kara da bayyana cewa, za a duba lafiyar daliba yayin tantancewar.

Ta kara da cewa, daliban su tafi da takardun shaidar karatunsu na ainihi tare da fotokwafi 15 na kowacce takardar, takardar shaidar haihuwa tare da takardar shaida daga karamar hukuma.

Akwai bukatar fasfoti 15, gajerun wanduna masu launin bula guda biyu, fararen riguna guda biyu, farin takalmi sau-ciki, safuna biyu, kwanonin cin abinci , kudin mota, da kuma katin duba jarabawar NECO, WAEC ko NABTEB.

Takardar ta kara da jaddada cewa, duk dalibin da bai zo da takardun ba, ba za a tantancesa ba.

Takardar ta kara da cewa, gwamnatocin jihohi su turo wakilansu don tantance takardar shaidar daliban jihohinsu. A don haka kuma ake bukatar iyaye da su kauracewa wajen tantancewar domin jami’ar ta tanadi wajen kwana da abinci ga daliban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel