Sojoji sun damke wasu da ke 'aiki' tare da 'yan Boko Haram a Borno

Sojoji sun damke wasu da ke 'aiki' tare da 'yan Boko Haram a Borno

Dakarun sojoji sun kama wani Usman Yage da ake zargi yana taimakawa 'yan ta'addan kungiyan Islamic State of West Africa (ISWAP) sayo masu kayayyaki da isar musu da sako a karamar hukumar Gubio na jihar Borno.

A cewar rundunar sojin Najeriya, binciken da aka fara gudanarwa ya nuna Yage wadda dan asalin kasar Chadi ne ya dade yana tattaunawa da kwamandojin ISWAP uku masu suna Goni Jere, Abul Qaqa da Modu Sulum.

Mai magana a yawun rundunar sojojin, Kwanel Aminu Iliyasu ya ce sojojin sun kama dan sakon 'yan ta'addan ne mai suna Alhaji Lawan a garin Maina Hari kamar yadda The Punch ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Tirkashi: Ba don doka ba, da na bindige mahaifi na har lahira, inji jarumi Dabo

Iliyasu ya ce, "Dakarun sojojin da aka kai Gubio sunyi nasarar dakile harin da 'yan ta'adda suka kai musu inda suka kashe dan ta'adda guda daya, suka kwato AK47 daya, carbin harashi daya, na'urar sadarwa da wayan tarho da kuma sirinji da da allurai.

"Kazalika, dakarun bataliya da 231 tare da hadin gwiwan 331 Artilllery Regimen sun sake kama wani mai yi wa 'yan ta'addan safarar kayayyaki, Alhaji Lawan yayin da ya ke kokarin wucewa da wasu kayan da ake kyautata zaton na 'yan ta'addan ne.

"Kayayakin sun hada da jarkokin man ja biyu, na man gyada biyu, katon din biskit, katon din taliya da pakitin maganin sauro 30.

"Sojojin hadin gwiwan sun kuma kama wani tsara wa 'yan ta'addan zirga-zirgan kayayyakinsu. Binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa Usman Yage dan asalin kasar Chadi ne kuma ya tade yana harka damanyan kwamandojin ISWAP Goni Jere, Abul Qaqa da Modu Sulum."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel