Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Yaro dan shekara 11 ya yiwa budurwa cikin shege har ta haihu

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Yaro dan shekara 11 ya yiwa budurwa cikin shege har ta haihu

- An kama wata budurwa da ta yiwa wani yaro fyade har ta kai ga ta sami ciki ta haihu

- Yanzu haka dai an yankewa budurwar hukuncin shekara 20 a gidan yari

- Yayin da shi kuma yaron wanda a yanzu haka yake da shekara 17 a duniya yake cigaba da rainon yaron na su

An tura wata mata gidan yari na tsawon shekara ashirin a birnin Florida, bayan an kamata da laifin yiwa yaro dan shekara 11 fyade har ta kai ga ta dauki ciki da shi.

Budurwar mai suna Marissa Mowry wacce keda shekaru 22, an dauke ta a matsayin wacce za ta dinga kula da yaron a shekarar 2014, inda ita kuma tayi amfani da wannan damar ta dinga lalata da yaron.

A yadda kotu ta bayyana, Marissa tayi lalata da wannan yaron ne a lokuta da dama ba tare da tayi amfani da wani abin kariya ba. A karshen shekarar 2014 din ta haifi jariri wanda yaron yayi mata cikin shi.

Sai dai yaron bai yi magana akan wannan abu ba sai a shekarar 2017, inda ya bayyanawa mahaifiyarsa, ita kuma ta tuntubi jami'an 'yan sanda, bayan anyi gwaji an gano cewa yaron shine mahaifin jaririn da Mowry take da shi sai aka kamata.

KU KARANTA: Bincike ya bankado cewa kudin da Cristiano Ronaldo yake samu a shafinsa na Instagram yafi wanda yake samu a kulob dinsa na Juventus

Yanzu haka dai Mowry tana da shekaru 28, inda shi kuma yaron yake da shekaru 17, shi kuma jaririn da suka haifa yanzu yana da shekara 5.

Mahaifiyar yaron da aka yiwa fyaden ta bayyanawa manema labarai cewa abinda Mowry ta yiwa danta ya canja mishi rayuwa baki daya.

Ta ce dan nata wanda a yanzu haka shima dalibi ne, sai ya fara kai dan da aka haifa masa makaranta a kowacc rana kafin shi kuma ya wuce tashi makarantar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel