Tirkashi: Ba don doka ba, da na bindige mahaifi na har lahira, inji jarumi Dabo

Tirkashi: Ba don doka ba, da na bindige mahaifi na har lahira, inji jarumi Dabo

Wani jarumin fina-finai mai karamin jiki, Samuel Dabo da aka fi sani da Yaw Dabo ya bayar da labarin yadda mahaifinsa ya yi watsi da shi da 'yan uwansa biyu da mahaifiyarsu da yadda ta sha wahalhalun kulawa da su ita kadai.

Acewarsa, mahaifinsa ya ya dawo daga baya ya nemi afuwarsa kuma ya nemi ya taimaka masa da kudi bayan ya fara samun karbuwa a sana'arsa na fina-finai.

Yawa ya bayyana cewa da yana da hali da ya bindige mahaifinsa har lahira a wannan lokacin.

DUBA WANNAN: Hotunan gangariyan sabbin jiragen kasa na zamani da China ta kera wa Najeriya

"Ni ne babban cikin 'ya'ya uku da mahaifanmu suka haifa kuma cikin izinin Allah dukkanmu munyi nasara a rayuwa bayan mahaifinmu ya tsere ya bar mu. Na yi kokari na gina wa mahaifiya ta gida mai dakuna uku kuma ina kulawa da ita duk da cewa abubuwa sun fara wahala a masana'antar fim," kamar yada Dabo ya fadi a wani shiri a gidan rediyon Nhyira FM mai suna Obra show.

Ya kara da cewa, "A cikin 'yan kwanakin nan mahaifiya ta ta kira ni tana neman in yafe wa mahaifina kuma in tallafa masa bayan ya fada mata cewa yana sha'awar irin baiwa ta da aikin da na ke yi a masana'antar fina-finai. Amma sai na tambayi kai na, shin zai nemi ni da 'yan uwa na idan bai gan ni a talabijin ba?"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel