NAF ta sake tarwatsa wani matattaran 'yan ta'addan Boko Haram a Borno

NAF ta sake tarwatsa wani matattaran 'yan ta'addan Boko Haram a Borno

Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta lalata wani matattaran 'yan ta'addan Boko Haram da ke Ngoske a kusa da dajin Sambisa a Borno inda ta kashe 'yan ta'adda da dama.

Direktan yada labarai na rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayar da wannan sanarwar a ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja.

Ya ce sashin mayakan sama dan ATF a karkashin atisayen Operation Lafiya Dole ne suka kai harin.

Ya ce, "An kai harin ne a yau 18 ga watan Oktoba bayan an kwashe kwanaki ana nazari da tattara bayanan sirri domin tabbatar da wuraren da gidajen 'yan ta'addan na Boko Haram suke da shugabaninsu da wurin taruwarsu."

DUBA WANNAN: Hotunan gangariyan sabbin jiragen kasa na zamani da China ta kera wa Najeriya

"Bayannan sirri da aka gano da na'urar ISR ta nuna cewa wasu gine-gine guda biyu ne 'yan ta'addan ke amfani da su domin haduwa su tattauna kafin su kaiwa dakarun sojoji ko al'umman gari hari.

"Kazalika, ATF ta tura dakarunta na sashin mayakan sama domin tawartsa matattaran 'yan ta'addan inda suka yi nasarar lalata gine-ginen biyu baki daya tare da kashe 'yan ta'adda da dama," inji shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta ce NAF ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin yunkurin ta na murkushe 'yan ta'addan da suka yi saura a yankin na Arewa maso Gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel