Yanzu-yanzu: An tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi, Achuba

Yanzu-yanzu: An tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi, Achuba

Ana saura wata daya gudanar da zaben jihar, an tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba.

Majalisar dokokin jihar sun tsige Mista Achuba ne a Lokoja, babbar birnin jihar, ranar Juma'a 18 ga Oktoba, 2019.

Shugaban masu rinjaye a majalisar ya bayyana hakan ne ga manema labarai a zauren majalisar.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Wani kwamitin binciken a kan zargin da ake yiwa mataimakin gwamnan Kogi Simon Achuba, wanda Barista John Baiyeshea ke jagoranta ya mika rahotonsa zuwa ga Majalisar jihar.

Alkalin alkalan jihar Kogi, Jastis Nasir Ajanah shi ne ya kafa wannan kwamitin. John kuma wanda shi ne shugaban kwamitin ya jagoranci mika rahoton binciken zuwa ga Kakakin majalisar jihar a ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba, 2019.

KARANTA: Kashi 14% na mutanen duniya masu shan 'Taramol' da 'Kodin' yan Najeriya ne - Binciken Janar Buba Marwa

Kakakin majalisar, Kolawole Matthew ne ya karbi rahaton daga hannun shugaban kwamitin a Majalisar jihar dake Lokoja.

Da yake magana bayan mika rahoton shugaban kwamitin ya ce sun yi iya bakin kokarinsu na yin bincike na gaskiya.

A cewar shugaban, John Baiyeshea, a shirye kwamitinsu yake domin amsa duk wata tambaya da ta shafi abinda rahoton nasu ya kunsa. Kuma ya kara da cewa rahoton ya kasu zuwa mujalladi uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel