Hoton wani matashin mawaki da budurwarsa sun jawo cece-kuce a tuwita

Hoton wani matashin mawaki da budurwarsa sun jawo cece-kuce a tuwita

- Hoton matashin mawakin nan mai suna Deezell da abar kaunarsa Jiddarh ya jawo kace-nace a kafar sada zumunta ta tuwita

- Mutane na ganin rashin dacewa ko aibun hoton ne ganin hausawa ne kuma musulmai 'yan arewa

- Mutane da dama sun dinga tunatar dasu koyarwar addini inda wasu kuma suka goyi bayansu

Wani matashin mawaki mai suna Deezell ya saka wani hotonsa da abar kaunarsa a shafinsa na tuwita don bayyanawa duniya yadda yake matukar kaunarta. Sai dai kash, hoton ya jawo cece-kuce a garesu.

A al'adar malam bahaushe, an sansa da kunya tare da kamewa. Amma sam ba a alakanta hoton da al'adar bahaushe ballantana kuma addini.

KU KARANTA: Zargin cin hanci: Akwai tambayoyin da zaka amsa, kotu tace wa Lawan

Idan aka gangara addini, saurayin da budurwar duk musulmai ne. Ana kuma sa ran sun san hukuncin taba namiji ko macen da ba muharramarka ko muharraminka ba.

Ganinsu hausawa kuma musulmai ne yasa ma'abota bin shafin saurayin suka yi caa akansa suna tunatar dashi azabar da zasu fuskanta matukar basu tuba ba.

"Annabi ya ce, zai fi ma mutum idan aka kafa masa kusa a kansa, akan ya tabi hannun macen da ba matarsa ba."

Wani kuma ya wallafa: "Ku gyara mu'amalarku kuma ku dena damunmu."

Ga abinda wani ya rubuta: "Zaka iya rike ko rungumar karfen da yayi ja a cikin wuta? Toh gara ka taba shi da ka taba macen da muharramarka ba."

Amma kuma sai aka samu wasu da suka kare masoyan. Sun zargi masu cece-kuce da munafinci don ba a san me suke aikatawa da masoyansu ba idan babu idon mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel