An karrama jarumi Ali Muhammad Nuhu a kasar Indiya

An karrama jarumi Ali Muhammad Nuhu a kasar Indiya

An karama shahrarren jarumin fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu a Indiya, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Rahoton ya bayyana cewa wasu dalibai Arewacin Najeriya da ke karatu a makarantar kiwon lafiya a kasar Indiya da malamansu Indiyawa ne suka gayyaci jarumin bikin Ranar Al'adu a makarantar.

An karrama jarumi Ali Muhammad Nuhu a kasar Indiya
An karrama jarumi Ali Muhammad Nuhu a kasar Indiya
Asali: Facebook

Ali Nuhu yace:

"Daliban na karanta fanni daban-daban kama daga fannin likita zuwa hada magunguna da injiniya da dai sauransu,"

"Akwai makarantar Dayananda Sagar School of Physiotherapy su ma sun ba ni lambar yabo kuma sun nuna jin dadinsu kan yadda daliban Najeriya ke mayar da hankali kan karatunsu."

"Wasu daga cikin malaman har fina-finan Hausa suke kallo saboda su ga yadda yanayin rayuwar Bahaushe ta ke."

"Shi ya sa idan wani dan wasa ya zo taro irin wannan su kan karrama shi,"

Ali Nuhu ya bayyana farin cikinsa da wannan karramawa da kuma yadda malaman wadannan makarantu ke da sha'awar al'adar Hausa.

A ranar Lahadi, 13 ga Oktoba, 2019, Ali Muhammad Nuhu, ya yanki tutar gwarzon diraktan shekara a taron bada lambar yabon City People Entertainment Awards na wannan shekaran.

Taron lambar yabon na aukuwa ne a kowani shekarar karkashin jagorancin mujallar City People ga jaruman Najeriya da Ghana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel