Ma'aikatan gwamnatin jihar Neja 4 sun mutu a mummunan hatsarin mota (Hotuna)

Ma'aikatan gwamnatin jihar Neja 4 sun mutu a mummunan hatsarin mota (Hotuna)

Ma'aikatan Kasa da Gidaje na Minna a jihar Neja a ranar Laraba 16 ga watan Oktoban 2019 ta rasa ma'aikatan ta hudu sakamakon mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su a hanyar Mokwa zuwa Batati.

Wadanda hatsarin ya ritsa da su sun hada da:

1. Ibrahim Audu (Jami'in tsare-tsaren gidaje a ofishin hukumar da ke Minna)

2. Ibrahim Babankogi (Jami'in Kasa a Mokwa)

3. Abubakar D Isah (Ofishin sufiyo a Mokwa)

4. Ya Idee (Ma'aikaci a ofishin ma'aikatar a Bida)

Ma'aikatan gwamnatin jihar Neja 4 sun mutu a mummunan hatsarin mota (Hotuna)
Ma'aikatan gwamnatin jihar Neja 4 sun mutu a mummunan hatsarin mota (Hotuna)
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

Kamar yadda hotunan hatsarin da shafin Linda Ikeja ta wallafa ya nuna, akwai alamar hatsarin ya afku ne sakamakon gaba da gaba da motarsu tayi da babban mota wadda hakan yasa motarsu tayi kundun bala bayanta kuma lotse.

Al'umma da dama sun garzaya inda hatsarin ya faru amma bisa ga dukkan alamu ba ayi nasarar ceto kowa daga cikinsu ba.

Hotunan sun nuna, jakarsu, takardunsu, fayafayan cd da sauran kayayaki daga cikin motarsu duk sun bazu a kan titi.

Daga bisani jami'an hukumar kiyaye haddura ta zihar sun hallarci wurin domin kawar da gawarwakin tare da kawar da motocin domin hana afkuwar cinkoson titi.

A yanzu dai babu wata majiya a hukumance da ta bayyana ainihin abinda ya yi sanadin afkuwar hadarin motar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel