Zakaran da Allah ya nufa da cara: An samu jariri da rai bayan kwana 2 da binnewa

Zakaran da Allah ya nufa da cara: An samu jariri da rai bayan kwana 2 da binnewa

A ranar Laraba ne likitoci suka ga wata 'karama' inda aka samu jaririya da ranta bayan kwanaki da binneta.

Jaririyar mai kwanaki 8 a duniya an sameta ne a tukunyar kasa a ranar Alhamis yayin da ake hakar kabari a wani kauye dake arewa da jihar Uttar Pradesh.

Diyar da bata isa haihuwa ba na da nauyin 1.1kg an garzaya da ita asibiti a mawuyacin hali.

"Mu'ujiza ce tasa har ta rayu duk da birneta da akayi," in ji Dakta Ravi Khanna.

Sannan ya kara da cewa, "An dade da birne jinjirar saboda kumatunta, wuyanta, cikinta da kafafunta duk sun rame."

A halin yanzu jaririyar ta ta fita daga mawuyacin halin bayan da aka saka ta a na'urar kyankyasa kuma tana cigaba da karbar magani.

"Muna shayar da ita madara ne kuma muna kara yawanta a hankali," Khanna ya ce.

DUBA WANNAN: Jakadan Najeriya ya bukaci a tsige gwamnan PDP a arewa, ya bayyana dalili

"Nauyin jinjirar ya karu daga yadda aka sameta kuma lafiyarta na samuwa a hankali."

Likitoci da 'yan sanda sun ce jaririyar na birne kusan kwanaki biyu ko sama da haka a cikin tukunya mai bula.

Jami'i mai jagorantar binciken, Pradeep Singh, ya ce, rundunarsu tana bincikar kauyukan kusa da inda aka tsinci jinjirar tare da tambayoyi akan masu juna biyu.

"Mun riga mun shigar da karar yunkurin kisa da neman salwantar da rayuwar da iyayenta da bamu gano ba suka yi," Singh ya sanar da AFP.

Ya ce za a mikata ga gidan raino na gwamnati bayan an sallameta daga asibiti.

Amma kuma wani dan siyasa na jam'iyya mai mulki, Rajesh Kumar Mishra, wanda ke biyan kudin maganinta ya ce zai rike yarinyar da yake kira da "karama".

"Kun taba tsammanin jaririya zata iya dadewa a cikin wannan ukubar? Ubangiji ne ya turota kuma na yanke shawarar riketa," Mishra ya sanar da AFP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel