Lambar yabo: Shugaban jami’ar ABU ya kere sa’anninsa a duk fadin Najeriya

Lambar yabo: Shugaban jami’ar ABU ya kere sa’anninsa a duk fadin Najeriya

Shugaban jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria, Farfesa Ibrahim Garba ne ya ciri tuta, kuma ya kere sa’a a duk fadin Najerya inda ya zamto zakaran gwajin dafi a tsakanin sauran shuwagabannin jami’o’in Najeriya na shekarar 2018.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito jaridar dake bin diddigin harkar ilimi a Najeriya ce ta sanar da haka a ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba, inda tace Farfesa Garba ya samu wannan lambar yabo ne sakamakon yadda ya kawo gyara a jami’ar cikin shekaru hudu.

KU KARANRA: Da dama daga cikin yan Najeriya basu iya wakar taken Najeriya ba – Minista Lai

Manajan mulki na kamfanin jaridar, Sameer S. Yusuf ne ya rattafa hannu a kan sanarwar, inda yace zasu karrama Farfesan da lambar girmama a wani taro da zasu shirya a babban birnin tarayya Abuja, wanda ake sa ran masu ruwa da tsaki zasu halarta.

“Sashin bincikenmu ne suka kaddamar da bincike tare da tambayoyi ga dalibai da malaman makarantu da dama, tare da al’ummomin da makarantun suke cikinsu don jin ra’ayinsu game da cigaban da shuwagabannin makarantun suka kawo a cikinsu.

“Daga karshen binciken, shugaban jami’ar ABU ya samu maki mai daraja 75 wajen kawo cigaba a makarantar, yayin da ya samu lambar yabo mai daraja ta ‘A’ wajen iya tafiyar da mulki a jami’ar.” Inji shi.

Daga karshe Sameer yace suna amfani da wannan ma’auni ne akan shuwgabannin jami’o’I, shuwagabannin kwalejojin ilimi, shuwagabannin kwalejojin kimiyya da fasaha na gwamnati da kuma masu zaman kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng