Da dama daga cikin yan Najeriya basu iya wakar taken Najeriya ba – Minista Lai

Da dama daga cikin yan Najeriya basu iya wakar taken Najeriya ba – Minista Lai

Ministan watsa labaru da al’adun gargajiya, Lai Mohammed ya bayyana cewa yan Najeriya da dama basu iya wakar taken Najeriya ba, watau National Anthen da Pledge, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Lai ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba yayin taron gabatar da tsarin bukatar canza salon tunani ga yan Najeriya don cigaban kasa, a turance Mindshift Advocacy for Development Initiative.

KU KARANTA: Rai banza: Dan damben boksin ya kashe abokin karawarsa da kwakkwaran naushi

Haka zalika Lai ya zargi yan Najeriya da dama da rashin girmama doka da oda, tare da yi ma kundin tsarin mulkin Najeriya karan tsaye. Ministan ya bayyana haka ne ta bakin daraktan ma’aikatar watsa labaru, Samuel Soughul.

Minista Lai ya cigaba da cewa duk kokarin da gwamnatin tarayya take yi na ganin ta karkatar da akalar kasar nan, amma akwai baragurbin mutanen dake kawo mata tasgaro. “Muna samun nasara, amma akwai wasu mutane a cikinmu da basu son ganin an samu cigaba.

“Bari mu fara daga kasa kasa, idan har kana kaunar kasarka, dole ne kaso duk wani abu dake da alaka da kasar, ya zama wajibi kaso jama’an kasar, ka so wakar taken kasar, amma yawancimmu basu iya wakar ba, ba zasu iya rubutata ba, kuma ba zasu iya rera wakar ba. Kai akwai matsala, amma kuma akwai haske a gaba.” Inji shi.

Daga karshe ministan ya karkare jawabinsa da cewa Idan zamu bi abubuwan dake cikin taken Najeriya, tabbas zamu daina ganin tashin hankali a gidajenmu, zamu daina amfani da motoci masu sulke, kuma yan Najeriya zasu so junansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel