An fara: Bayan maganar Sabo Nanono, Wani yaci abincin N150 ya rantse N30 zai biya (Bidiyo)

An fara: Bayan maganar Sabo Nanono, Wani yaci abincin N150 ya rantse N30 zai biya (Bidiyo)

Wani faifan bidiyo dake yawo a shafukan ra'ayi da sada zumunta na nuna wani matashi a wata jihar Arewa da ya sayi abinci hannun yarinya a kasuwa amma yaki biyan kudin da ya kamata.

Matashin ya ci abincin N150 amma ya lashi takobin cewa N30 zai biya.

Wannan ya biyo bayan jawabin ministan noma, Sabo Nanono, inda ya ce N30 zai kosar da mutum a jihar Kano.

Sabo Nanono ya ce Najeriya a noma abinci mai yawan gaske da zai iya ciyar da kasar baki dayanta, sabanin labarin da wasu ke yadawa na cewa akwai yunwa a wasu bangarorin kasar.

Nanono ya fadi wannan maganar ne a Abuja ranar Litinin 14 ga watan Oktoba, 2019 a lokacin da yake cigaba da shirye-shiryen bikin ranar abinci ta duniya da ta kama 16 ga watan Oktoba.

Yace: “Zan iya cewa muna noma abinda zam ci kuma babu yunwa a kasar nan, amma dai idan kuka ce ‘yar tangarda da ba’a rasa ba zan yadda gaskiya. Abinci a Najeriya yana da matukar arha sosai fiye da sauran kasashen duniya.

“A Kano zaka iya cin abinci da naira 30 kacal kuma ka koshi. A ganina kamata yayi mu godewa Allah da ya bamu ikon noma aboncin da za mu iya ciyar da kanmu kuma babu tsada a kasar nan.” Inji Ministan.

Kalli bidiyoyin:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel