'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba

'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba

Najeriya kasa ce da ke da 'yan kwallon kafa masu baiwa sosai da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba.

Hakan na faruwa ne saboda kasancewarsu masu izinin zama a kasashe biyu, ra'ayin kansu ko kuma rashin samun damar buga wa kasarsu ta haihuwan kwallo.

Ga jerin sunayen wasu 'yan wasan masu hazaka da ba su taba buga wa Najeriya kwallo ba:

DUBA WANNAN: Wani mutum ya 'mutu' ya dawo bayan shekara 30 a Kano

1. David Alaba

'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba
David Alaba
Asali: Twitter

An haifi David Olatokunbo Alaba ne a Vienna, mahaifiyarsa ma'aikaciyar jinya ce 'yar kasan Philipine yayin da mahaifinsa dan Najeriya ne mawaki. Yana buga wa kasar Australia kwallo kuma ya na bugawa kungiyar Bayern Munich.

2. Gabriel Agbonlahor

'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba
Gabriel Agbonlahor
Asali: Twitter

An haifi Gabriel Imuetinyan 'Gabby' Agbonlahor a ranar 13 ga watan Oktoban 1986. Mahaifiyarsa 'yar kasar Scotland ne yayin da mahaifinsa kuma dan Najeriya ne. Ya na buga wa kungiyar Aston Villa kwallo.

3. Nedum Onuoah

'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba
Nedum Onuoah
Asali: Twitter

Chinedum “Nedum” Onuoha dan kwallo ne da ke bugawa Real Salt Lake kwallo. An haifi shi a birnin Warri a Najeriya amma ya girma a Manchester a kasar Ingila.

A 2007, Najeriya ta gayyaci shi don ya buga mata wasa amma ya ce kasar Ingila zai buga wa kwallo. Sai dai duk da hakan Ingila ba ta taba saka shi buga mata wasa ba.

4. Ross Barkley

'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba
Ross Barkley
Asali: Twitter

An haifi Ross Barkley a ranar 5 ga watan Disamban 1993. Ya girma a birnin Liberpool amma kakansa a bangaren mahaifi 'dan Najeriya ne hakan ya bashi damar buga wa Najeriya ko Ingila kwallo.

Daga bisani ya zabi kasar Ingila kuma ya buga wasa kasa da shekaru 16, 17, 19, 20, 21 da kuma babban kungiyar kwallo ta Ingila.

5. Emmanuel Adebayor

'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba
Emmanuel Adebayor
Asali: Twitter

Iyayen Emmanuel Adebayor asalinsu 'yan Najeriya ne amma suka koma kasar Togo da zama. Ya bugawa kungiyar İstanbul Başakşehir na kasar Turkiyya kwallo. A baya ya buga wa kungiyoyi kamar Arsenal, Manchester City, Tottenham Hotspur da Crystal Palace da kuma Metz da Monaco da Real Madrid.

An zabe shi a matsayin dan kwallon Afrika ta shekarar 2008.

6. Patrick Olukayode Owomoyela

'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba
Patrick Olukayode Owomoyela
Asali: Twitter

Mahaifiyar Patrick Olukayode Owomoyela 'yar kasar Jamus ne amma mahaifinsa 'dan Najeriya ne. Yana cikin tawagar kwallon kafa na Jamus da suka buga Kofin Confederations ta FIFA 2005. A yanzu ya dena taka leda ya zama dan jarida na wasanni.

7. Angelo Ogbonna

'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba
Angelo Ogbonna
Asali: Twitter

Angelo Obinze Ogbonna dan kwallon kasar Italiya ne da ke buga tsakiya ta baya a kungiyar West Ham da kuma kungiyar kasar Italiya.

Iyayensa haifafun 'yan Najeriya ne amma daga baya suka yi hijira zuwa kasar Italy a 1983.

8. Stefano Okaka Chuka

'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba
Stefano Okaka Chuka
Asali: Twitter

An haifi Stefano Okaka Chuka ne a Castiglione del Lago, Perugia a kasar Italy amma iyayensa biyu duk 'yan Najeriya ne daga baya suka samu izinin zama 'yan kasar Italiya. Okaka ya shiga kungiyar kwallo ta yara na Roma a 2004.

Daga bisani ya samu shiga kungiyar kwallon kafa ta kasar Italy kuma a yanzu yana buga wa kungiyar Parma kwallo duk da cewa sun bayar da aronsa ga Spezia Calcio.

A 2014, Okaka ya ce yana tattaunawa da Kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya NFF kan yiwuwar buga wa Najeriya kwallo a kofin duniya ta FIFA 2014.

9. Dennis Aogo

'Yan kwallon kafa 9 'yan Najeriya da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba
Dennis Aogo
Asali: Twitter

Mahaifin Dennis Aogo dan Najeriya ne amma mahaifiyarsa 'yar kasar Jamus ne. Dan kwallon dan shekaru 30 ya taba fadin cewa Najeriya ta gayyaci shi ya buga wa Super Eagles kwallo amma bai amsa kirar ba.

Ya ce, "Da naji Najeriya tana son in buga mata wasa, na zauna na yi tunani amma ban amince ba don 'yan Najeriya ba za su amince da ni a matsayin asalin dan Afirka ba. Rayuwarsu ta banbanta da abinda na saba da shi a Jamus.

"Na san akwai 'yan Afirka da yawa da aka haifa a Turai da ke bugawa kungiyoyin Afirka kwallo amma ba a daukan su a matsayin 'yan kasa. Najeriya ba ta da tsari kamar yadda Jamus ke da shi. Na taba zuwa Najeriya na yi kwanaki 14 saboda haka na san abinda na ke so."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel