Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin sakin N10bn don ginin filin jirrgin Enugu

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin sakin N10bn don ginin filin jirrgin Enugu

Labari da duminsa daga fadar shugaban kasa na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin sakin naira bilyan goma ga yankin kudu maso yammacin Najeriya domin ginin filin jirgin saman Enugu.

Buhari ya bayyana hakan yayinda shugabannin kabilar yankin wanda ya hada da kungiyar Ohaneaze Ndiigbo da gwamnonin jihohin biyar suka kai masa ziyara a yau Alhamis, 17 ga Oktoba, 2019.

Buhari ya jaddada niyyar inganta ayyukan gine-gine a Najeriya domin jin dadin al'ummar kasar.

Shugaban kasan yace: "Na bada umurnin sakin Bilyan 10 domin inganta ginin babbar filin jirgin saman Akanu Biam dake jihar Enugu. Ministan sufurin jirgin sama ya bani tabbacin cewa za'a yi gaggawan kammala aikin kuma mai kyau."

"Duk da cewa muna da abubuwa da yawa da muke son yi kuma babu kudi, za mu cigaba da gaggauta yin manyan ayyuka a dukkan sassan kasa. Aikinmu ne mu tabbatar an gyara dukiyoyin kasa. Ba zamu gajiya ba"

Mun kawo muku rahoton cewa Gwamnonin yankin kabilar Igbo ta kudu sun shiga ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa, Aso VIlla, birnin tarayya Abuja.

Daga cikin gwamnonin sune Okezie Ikpeazu (Abia), Emeka Ihedioha (Imo), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu) da Gwamnan jihar Anambara, Willie Obiano, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa.

Sauran sune gwamnan jihar Bayelsa, Henry Seriake Dickson; Gwamna Nyesom WIke na River; mataimakin Edo, Philip Shaibu da gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel