An dakatar da wata mata mai shekaru 36 daga haihuwa bayan ta haifi 'ya'ya 44

An dakatar da wata mata mai shekaru 36 daga haihuwa bayan ta haifi 'ya'ya 44

A karshe dai likitoci sun samu hanyar hana Mariam Nabatanzi haihuwa.

Asalin 'yar kasar Uganda mai shekaru 35 tana da 'ya'ya 44 a duniya ta haifa 'yan biyu sau hudu, 'yan uku sau biyar da 'yan hudu sau biyar.

Nabatanzin wacce a halin yanzu bata da aure na dinki, gyaran kai da sayar da magungunan gargajiya don samun abinda zata ciyar da yaranta 38.

An ruwaito cewa, ta yi aure a lokacin da take da shekaru 12 da namiji mai shekaru 40 a duniya.

An dakatar da wata mata mai shekaru 36 daga haihuwa bayan ta haifi 'ya'ya 44
An dakatar da wata mata mai shekaru 36 daga haihuwa bayan ta haifi 'ya'ya 44
Asali: Twitter

Ta fara haihuwa ne da shekara daya bayan aurenta.

"Ina kokarin basu ilimi. Fatana kullum shine suje makaranta. Zan iya hanasu komai, amma sai sunje makaranta,"

"Bazan iya cewa sun takura ni ba sabda 'ya'yana ne. Ba zan ce zan barsu ba saboda 'ya'yana ne kuma ina sonsu," Nabatazni ta fadi.

An dakatar da wata mata mai shekaru 36 daga haihuwa bayan ta haifi 'ya'ya 44
An dakatar da wata mata mai shekaru 36 daga haihuwa bayan ta haifi 'ya'ya 44
Asali: Twitter

Ta tuna cewa, akwai likitan da ya ja mata kunne akan shan kwayar hana daukar ciki. Zasu iya jawo mata matsala sakamakon girman kwayayen haihuwarta. Bayan kuwa haihuwar 'yan biyunta na farko, sai ta cigaba da zazzagosu.

Jaridar Mirror ta ruwaito cewa, Nabatazni na da shekaru 23 amma ta mallaki yara 25 . A lokacin ne kuma ta fara rokon likitanta da ya taimaka mata ta daina haihuwa. Amma kash, likitan ya sanar da ita cewa zai fi amfani idan ta cigaba da haihuwa.

Haihuwarta ta karshe inda ta haifa 'yan uku kashi na shida tazo da matsala. Daya daga cikin jariran ya mutu kuma mijinta da kan yi tafiyar satittika ya tsere gaba daya.

Mariam ta ce: "Na rayu cikin kunci, mijina ya barni a wahala. Duk kokarina yana kan kula da yara na."

Bayan wannan haihuwar ne ta samu tallafin likita inda aka sanar da ita yakamata ta daina haihuwa. Ta ce, "Likitan ya sanar dani cewa ya cire min mahaifa".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel