A tunanina akuya na kashe, in ji mijin da ya kashe matarsa

A tunanina akuya na kashe, in ji mijin da ya kashe matarsa

- Hukumar 'yan sanda ta jihar Ondo ta gurfanar da wani magidanci gaban kotu sakamakon zarginsa da take da hallaka matarsa, uwar 'ya'yansa

- Magidancin mai shekaru 63 a duniya ya sanar da kotun cewa, shi dai kukan akuya yaji yayin da yake sassara matarsa gaba-gaba da adda

- Ya roki kotun da tayi masa rangwame don kuwa shi a tunaninsa akuya yake kashewa lokacin da yake halaka matarsa

Oluwatubosun Dahunsi, wanda aka gurfanar a gaban babban kotun majistare da ke Akure, yace bai san me ya shiga ransa ba har ya kashe matarsa Oluwafunmilayo.

Hukumar ‘yan sanda jihar Ondo ta kama Oluwatubosun ne sakamakon zarginsa da ake da kashe matarsa a Ita-Ipele a karamar hukumar Owo ta jihar a ranar 6 ga watan Oktoba, 2019.

Manomin mai shekaru 63 a duniya ya hallaka matar tasa ne da adda.

Wanda aka gurfanar din ya musanta aikata hakan a gaban kotu.

KU KARANTA: Kotu ta bukaci tsare malamin gidan horo na Daura tare da wasu mutane biyu a gidan yari

Zargin da ake masa ne kamar haka, “Cewa kai Oluwatubosun Dahunsi, a ranar 5 ga watan Oktoba, 2019, wajen karfe 6;30 na safe a sansanin Ita-Ipele da ke karamar hukumar Owo ka daddatsa matarka, Oluwafunmilayo da adda wanda yayi sanadin rayuwarta. Hakan kuwa ya ci karo da sashi na 319, sakin layi na daya na crimal code na jihar Ondo.”

Oluwatubosun, wanda bai da lauya mai wakiltarshi, ya sanar da kotun cewa, ya dawo cikin hankalinsa ne bayan ya gama aika-aikar. Ya ce, kisan yayi shi ne kan kuskure kuma yana rokon rangwamen kotun.

“Mun samu hargitsi ne da ita akan kudin makarantar yaranmu. Bansan lokacin da na fara sarata da addar ba. Bayan ta mutu ne na dawo hankalina,’ in ji shi.

Da kotun ta tambayeshi ko matar tasa bata yi ihun neman taimako ba, sai ya ce, “Tayi ihu gaskiya amma sai naji tamkar kukan akuya ne. A don haka ne nayi tunanin akuya nake kashewa. Bayan na gama ne na gane ita na kashe shine daga baya na nemi wajen gudu.”

Alkalin ya bukaci a adana magidancin a gidan gyaran hali har zuwa 13 ga watan Janairu na 2020 da za a dawo kotu don cigaba da shari’ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel