'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

- Kungiyar Autochthonous Persons of Jos (APJ) tayi Allah-wadai da nadin mukamin da Gwamna Lalong ya yi wa Shehu Bala

- Kungiyar ta 'yan asalin jihar Filato ta ce nadin da aka yi wa bare wanda ba dan asalin jihar ba ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa da ka'idojin demokradiyya

- Kungiyar tayi gargadin cewa irin wannan nadin wadda ba bisa ka'ida ba yana iya janyo barkewar rikicin a jihar

Wata kungiya ta al'umma 'yan asalin jihar Filato (APJ) tayi Allah wadai da nadin da Gwamna Simon Lalong ya yi wa wani mutum wanda ba dan asalin jihar ba kuma dan jam'iyyar APC, Shehu Bala a matsayin ciyaman din kwamitin kulawa da karamar hukumar Jos ta Arewa.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An tsinto wasu iyali da suka kebe tsawon shekaru 9 suna jiran 'karshen duniya'

Sahara reporters ta ruwaito cewa mai magana da yawun APJ, Theresa Azi Nyako a yayin taron manema labarai a ranar Talata ya ce, "Muna son mu bayyana cewa kwata-kwata ba mu amince ba kuma munyi tir da danne mana hakokinmu a karamar hukumar Jos ta Arewa da ma wasu saurarn abubuwa.

"Kakakba mana wanda ba asalin dan karamar hukumar mu ba kuma tsohon dan takarar jam'iyyar APC yayin zabe ya sabawa dukkan ka'idojin yadda ake demokradiyya a duniya, hakan haramun ne, sabawa doka ne kuma ya ci karo da tanadin kundin tsarin mulki.

"Wannan rashin adalci ne ga al'ummar mu musamman 'yan asalin jihar Filato kuma hakan na iya kawo tashin hankali a birnin ta Jos. Hakan ya sabawa tsarin gwamnan na 'three point agenda.'"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel