Jigawa: Shugaban makarantar sakandare ya rasa aikinsa saboda satar kwamfuta

Jigawa: Shugaban makarantar sakandare ya rasa aikinsa saboda satar kwamfuta

Ma'aikatan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar Jigawa ta sallami Shugaban makarantar Unity Sakandare ta Maigatari, Dayyabu Madaki a kan sakaci da aikinsa.

An bayana korarsa ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Yakubu Abbas, sakataren dindindin na ma'aikatar da ya Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ta samu a Maigatari a ranar Laraba kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mista Abbas ya ce korar da aka yi wa Mista Madaki zai zama hukuncin kan sace kwamfuta kirar K-Yan da ake amfani da shi wurin koyar da dalibai da aka ce ba a san wanda ya sace ba.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An tsinto wasu iyali da suka kebe tsawon shekaru 9 suna jiran 'karshen duniya'

Ya ce wannan sakaci ne kuma ba zai yi wa ayi masa afuwa ba 'saboda ma'aikatar da umurci dukkan shugabannin makarantar su rika saka idanu kan kayayyakin koyarwa da aka damka amana a hannunsu.'

Sakataren da dindindin ya ce ofishin Ilimi na ma'aikatar da ke Gumel za ta rika kulawa da makarantar a halin yanzu.

NAN ta ruwaito cewa ya ce an mayar da shugaban makarantar da aka tsige daga mukaminsa zuwa ma'aikatar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel