Kishin-kishin: Real Madrid za ta maye gurbin Gareth Bale da dan kwallon Super Eagles

Kishin-kishin: Real Madrid za ta maye gurbin Gareth Bale da dan kwallon Super Eagles

- An samu wasu rahotanni da suka ce kungiyar Real Madrid tana shirin maye gurbin Gareth Bale da Samuel Chukwueze

- Dan kwallon Najeriyan yana da damar barin kungiyarsa ta Villarreal idan har za a iya biyan £63m

- Chukwueze ya jefa kwallaye biyu a raga cikin wasanni bakwai da ya buga wa Villareal

Babban kungiyar kwallo ta Real Madrid suna kokarin maye gurbin tauraron kasar Wales Gareth Bale da buga gefe na Super Eagles Samuel Chukwueze.

A cewar shafin Fichajes na kasar Spain, an yi ta kokarn mayar da Bale zuwa Manchester United bayan yunkurin mayar da shi wata kungiyar kasar China Jiangsu Suning bai yi wu ba a kasuwar sayar da 'yan wasa na bara.

Rahoton ya yi ikirarin cewa akwai yiwuwar dan wasan na Najeriya zai bar Villareal a karshen kakan wasa ta 2109 zuwa 2020 duba da cewa kungiyoyi da dama suna nemansa ciki har da kungiyar Real Madrid.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An tsinto wasu iyali da suka kebe tsawon shekaru 9 suna jiran 'karshen duniya'

Chukwueze ya bugawa Golden Eaglet wasa a gasar cin kofin duniya na 'yan shekaru kasa da 17 na 2015 kuma daga bisani kungiyar Villareal ta saye shi bayan ya cika shekaru 18 a watan Augustan 2017.

Legit.ng a baya ta ruwaito cewa kungiyar Barcelona tana shirin sayan Chukwueze idan ba ta samu sayan Neymar daga Paris Saint-German a watan Janairu kamar yadda wata rahoto tayi ikirari.

A cewar Gol Digital, kungiyar ta Real Madrid tana son sayan Chukwueze idan har ba ta samu Neymar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel