Jerin sabbin dokoki 5 da shugaba Buhari yasa hannu

Jerin sabbin dokoki 5 da shugaba Buhari yasa hannu

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu a kan sabbin dokokin da majalisar dattawa ta aminta dasu guda biyar

- Dokokin zasu tabbatar da shugabanci mai kyau a kasar nan ne kamar yadda mai bada shawara ga shugaban kasa akan harkokin majalisar dattawa ya sanar

- Dokar ta hada da karancin matakin karatun da shugaban majalisar zartarwar jami'a zai mallaka kafin hya iya hawa matsayin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu akan sabbn dokokin da majalisar datttawa ta aminta dasu guda biyar.

Umar Yakubu, babban mai bada shawara ga shugaban kasa akan harkokin majalisar dattawa ya sanar da hakan.

Yakubu, wanda ya yi sanarwar a taron manema labarai a ranar Laraba a Abuja, ya ce, an yi dokokin ne don tabbatar da shugabanci mai kyau a kasar.

KU KARANTA: Ahmed Aliyu da jam'iyyar APC sun daukaka kara akan hukuncin zaben jihar Sokoto

Dokokin sun hada da, gyararrun dokokin jami’ar Obafemi Awolowo, jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, jami’ar Maiduguri, dokar nagartar taki ta kasa da sauransu.

Gyararrun dokokin jami’o’in sun hada da karancin shaidar digirin farko ko makamancinsa ga wanda zai jagoranci hukumar zartarwa ta jami’o’in.

Yakubu Yace, dokar ta ce, duk wanda zai yi jagorancin dole ya kasance ba mai nakasa ba don ya iya rike al’amuran shuagabncin. Dokar ta kara da cewa, duk wani dalibi ko malami da zai gurfanar da jami’o’in, dole ya sanar da hukumar a kalla ana sauran wata daya.

Dokar nagartar takin ta kasa ita kuma anyi ta ne don kare hakkin manoma da kuma kawo karshen karancin sinadarai da yakamata taki ya kunsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel