Ku bude mana boda tun da bamu rufe namu ba - Kasar Ghana ta bukaci Najeriya

Ku bude mana boda tun da bamu rufe namu ba - Kasar Ghana ta bukaci Najeriya

Ministar harkokin wajen kasar Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey, ta bukaci gwamnatin Najeriya ta taimakawa ta bude iyakarta saboda kayayyakin kasar su rika jiga Najeriya.

Za ku tuna cewa tun watan Agusta, gwamnatin tarayya ta kulle dukkan iyakokinta domin dakile safarar makamai da shinkafa.

Yayinda take ganawa da jakadan Najeriya a Ghana, Olufemi Abikoye, ministar ta ce har yanzu kayayyakin Najeriya na shiga Ghana.

Ta ce gwamnatin Ghana za tayi amfani da dukkan wani faka ta diflomasiyya domin tabbatar da cewa Najeriya ta bude iyakokinta ga kasashen dake makwabtaka da ita domin shigowan kayayyaki.

KU KARANTA: An kona motoci 9 makare da Kifi da akayi yiwo safarasu daga kasar Nijar

Ministar ta ce yan kasuwa a Ghana sun yi mumunan fadi sakamakon rashin shigowar kayayyakinsu Najeriya ta Seme.

Tace: "A yanzu da nake magana, kayayyakin Najeriya na shiga Ghana ba tare da fuskantar wani matsala ba kuma ina ganin ya kamata a nemi wasu hanyoyi magance matsala da kasashen kuke da matsala da su saboda kayayyakin Ghana sun iya shiga kasarku ba tare da matsala ba."

Abikoye ya tabbatarwa ministar cewa Najeriya zata hada kai da Ghana wajen neman mafita daga cikin wannan lamari.

Ya ce ba kasar Ghana akayi nurfin cutarwa da kulle iyakokin ba, amma mataki ne da aka dauka domin inganta tattalin arzikin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel