Me yayi zafi? Ta kona mazaunan masu aikinta da dutsen guga

Me yayi zafi? Ta kona mazaunan masu aikinta da dutsen guga

- Ana zargi wata mata mai suna Alhaja Baliqees Yahyah Muhammad da laifin cin zarafin masu aikinta guda biyu

- Wani ma'abocin amfani da Facebook ya wallafa hoton matar da mazaunan 'yan aikinta nata masu kananan shekaru da ta kona da dutsen guga

- Duk da hukumar NSCDC na kan lamarin, ya bukaci lauyoyi masu rajin kare hakkin bil adama, kungiyoyin sa kai da 'yan kasa nagari da su shiga lamarin

An zargi wata mata mai suna Alhaja Baliqees Yahyah Muhammad da laifin amfani da dutsen guga mai zafi wajen kona mazaunan masu aikinta da ke da kananan shekaru.

Lamari ya faru ne a Ilorin, babban birnin Kwara a ranar 11 ga watan Oktoba. An gano cewa Hauwa mai shekaru 9 da Aisha mai shekaru 12 suna aiki da matar.

KU KARANTA: Tirkashi: Wani mutum mai 'ya'ya 100 ya auro mata 4 don bukatar karin haihuwa

A halin yanzu, hukumar NSCDC na bincikar al’amarin.

Ma’abocin amfani da kafar sada zumunta ta Facebook mai suna Abdulhakim Abdulkadir ne ya wallafa hoton a shafinsa tare da tsokaci kamar haka: “Abun kamar almara. Da gangan uwar dakinsu tayi amfani da dutsen guga wajen kona musu mazaunai. Abin ya faru ne a ranar Juma’a, 11 ga watan Oktoba ga yara kanana masu shekaru 9 da 12,”

Muna kira ga lauyoyi masu rajin kare hakkin bil adama, kungiyoyin sa kai da kuma ‘yan kasa nagari dasu kawo dauki ga yaran nan tare da kwatar musu hakkinsu a wajen matar nan. Sunan muguwar matar, Alhaja Baliqees Yahyah Muhammad. Su kuma masu aikin sunansu Hauwau da Aisha.” In ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel