Za’a yanke albashin duk masu mukaman siyasa don biyan karancin albashi – Minista

Za’a yanke albashin duk masu mukaman siyasa don biyan karancin albashi – Minista

A kokarinta na ganin ta iya biyan sabon karancin albashin N30,000 ga ma’aikatan Najeriya, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai yiwuwar za ta zaftare albashi da kuma alawus alawus na masu rike da mukaman siyasa a duk fadin kasar.

Jaridar The Cables ta ruwaito ministan kwadago, Chris Ngige ne ya bayyana haka yayin da wakilan kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta NULGE suka kai masa ziyara a ofishinsa a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Rikicin cikin gida: Ta tabbata Buhari ba zai iya rike gidansa ba balle Najeriya – PDP

“Rage albashin ma’aikata da aka yin a karshe an yi shi ne a shekarar 2011, kuma a yanzu ma muna shirin sake yin wani, tuni gwamnati ta kafa wata kwamiti da za ta duba albashin masu rike da mukaman siyasa, inda ta nada ministan kudi da kuma ni a matsayin shuwagabannin kwamitin.” Inji shi.

Ministan yace kwamitinsu zai yi duba ga tsarin albashi na 12 da Najeriya ke amfani da shi, sa’annan ya kara da cewa zasu rage albashin duk wani mai rike da mukamin siyasa, ciki har da gwamnoni.

“Akwai mutanen dake karbar kashi 300 na albashin da wasu ke karba duk da cewa dukkaninsu digiri ce suke dashi, akwai mutanen dake aiki a NNPC, FIRS, Kwastam da wasu hukumomi dake da digiri mai daraja ta uku (Third Class) amma kuma suna amsan kashi 300 na albashin mai digiri mai daraja ta daya (First Class) dake aiki a wata ma’aikata

“Haka zalika hukumar tattara kudaden gwamnatii za ta duba abin da ake biyan masu rike da mukama siyasa, misali, me gwamna yake yi da alawus din hadari? Wani hadari yake ciki alhali jahar c eke ciyar dashi da iyalinsa?

“Me gwamna ke yi da kudin mazaba? Bayan dukkanin jahar ce mazabarsa? Wadannan na daga cikin abubuwan da zamu yi duba a garesu da idon basira.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel