Boko Haram na samun tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu – Sanata Ndume

Boko Haram na samun tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu – Sanata Ndume

Wakilin yankin mazabar Borno ta kudu a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa akwai wasu kungiyoyi masu zaman kansu dake fakewa da aikin bayar da tallafi ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a jahar Borno, amma suna taimaka ma kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Sanatan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a majalisar dattawa a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba, a matsayinsa na shugaban kwamitin majalisar dake kula da rundunar Sojan kasa.

KU KARANTA: Gwamnati na kokari wajen samar da tsaro, amma ba’a gani – Minista

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ndume yace ya samu wannan bayani ne bayan dawowa daga ziyarar daya kai jahar Borno a kwanakin baya, inda yace tabbas ta tabbata akwai hannun wasu kungiyoyi masu zaman kansu dake baiwa yan Boko Haram kayan aiki.

“Wani lamari da zamu duba shi ne zarge zargen da ake yi ma kungiyoyi masu zaman kansu daban daban game da taimaka ma Boko Haram ta hanyar basu bayanan sirri, kayan aiki da dai sauransu. Na dade ina nuna damuwa game da haka, kuma jama’a na gargadina game da hakan.

“Amma a yanzu ta tabbata akwai wasu kungiyoyi biyu zuwa daya da akwai tabbacin suna baiwa Boko Haram tallafi tare da goyon bayansu, amma zamu gudanar da bincike, kuma za’a ji idan muna da hujjoji. Zuwa yanzu dai muna da hujjoji.” Inji shi.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne rundunar Sojan Najeriya ta kaddamar da samame a kan wasu kungiyoyi masu zaman kansu bisa tuhumarsu da take yi da taimaka ma mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel