Tsaro ya fi bin doka da hakkin dan adam muhimmanci - Hameed Ali
Shugaban Kwastam ta Najeriya, Hameed Ali ya ce 'yan Najeriya su manta da batun wasu dokokin kasa da hakokin dan adam a wuraren da ake neman tabbatar da tsaro.
Premium Times ta ruwaito cewa matsayar da Mista Ali tayi kamanceceniya da ta Shugaba Muhamamdu Buhari da Attoney Janar na kasa Abubakar Malami wadanda duk suka bayyana cewa tsaro yana kan gaba da sauran dokokin kasa.
A yayin jawabin da ya yi wa manema labarai yayin rufe iyakokin kasa a ranar Litinin, The Nation ta ruwaito cewa Ali ya ce "Babu wani doka ta tafi samar da tsaro muhimmanci."
DUBA WANNAN: Zaben Kogi: Hotunan Wada yana sharbar barci a wurin taro ya karade shafukan sada zumunta
"Muna son mu tabbatar cewa mun kiyaye al'ummar mu. Mai rai ne kawai ya ke iya neman hakkinsa. Kana da hakoki ne idan kana raye.
Wata jarida na Legas ta ruwaito shugaban na kwastam na cewa, "Ku je ku tambayi mutane a Maiduguri lokacin da Boko Haram ke yi wa rayyukansu barazana, abinda ke zukatansu kawai shine yadda za su tsira da ransa ba wai batun hakoki ba. A yanzu ma, dole Najeriya ta tsira da ranta kafin mu fara maganan hakoki."
A ranar Litinin din, Mista Ali ya ce iyakokin kasar za su cigaba da kasancewa a rufe kamar yadda aka fara rufe wasu tun a watan Augusta.
Ya ce an dauki matakin ne domin inganta tattalin arzikin Najeriya da kuma rage yadda kasashen da ke makwabtaka da Najeriya ke zaluntar kasar kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng