Jerin sunaye: Mutum 5 da suka taba lashe kyautar Nobel a Afirka

Jerin sunaye: Mutum 5 da suka taba lashe kyautar Nobel a Afirka

Wole Soyinka, Nelson Mandela da wasu mutane uku na daga cikin 'yan Afirka ta aka karamma da lambar yabo ta Nobel tun da aka kirkiri shi a 1901. Ana bayar da kyautan na Nobel na ga mutanen da suka bayar da muhimmiyar gudunmawa domin inganta rayuwan al'umma.

'Yan Afirka biyar da suka samu kyautan ta Nobel a lokuta daban-daban duk kwararru ne a ayyukansu da suka hada da mulki na gwamnati, fafutikan kwato wa al'umma hakkinsu da sauransu.

Ga jerin mutanen da suka taba lashe kyautan na Nobel.

1. Wole Soyinka

Shine dan Afirka na farko da ya fara samun lambar yabon a 1986 saboda fasaharsa a fanin rubutu. Soyinka wadda aka haifa a 1934 ya cigaba da kasancewa cikin masu fada a ji a fannin rubuce-rubuce a Najeriya.

Ya yi karatunsa a gida Najeriya da kuma kasar Ingila. Ya kware a fanoni daban-daban na rubutu. Wasu daga cikin litaffan da ya rubuta sun hada da Trials of Brother Jero da A Voyage Around Essay.

2. Wangari Maathai

An haife ta a ranar 1 ga watan Afrilun 1940. Mathaai 'yar kasan Kenya ce kuma tana matukar kulawa da muhalli. Ta kasance 'yar gwagwarmaya ce kan hakokin mata da kare muhalli ta hanyar amfani da wata kungiya da ake kira Green Belt Movement. Ta samu lambar yabon a 2004.

Jerin sunaye: Mutum 5 da suka taba lashe kyautan Nobel a Afirka
Jerin sunaye: Mutum 5 da suka taba lashe kyautan Nobel a Afirka
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Zaben Kogi: Hotunan Wada yana sharbar barci a wurin taro ya karade shafukan sada zumunta

3. Nelson Mandela

Shugaban kasar Afirka ta Kudu na farko a 1994 kuma shine kan gaba wurin yaki kan tauye hakokin mata. Ya samu lambar yabon tare da Frederik Willem ke Klerk a 1993 saboda gwagwarmayar da suke yi kan nuna banbancin launin fata a Afirka ta Kudu.

Mandela ya mutu a 2013 kuma an masa jana'iza ta ban girma wadda shugabanin duniya da dama suka hallarta.

4. Kofi Annan

Shine sakatare janar na majalisar dinkin duniya tsakanin 1997 zuwa 2006. An haife shi a Ghana a 1938 kuma kwararre na a nazarin tattalin arziki. Ya karbi kyautan a 2001 saboda himmarsa wurin kokarin kwato hakkin dan adam.

5. Albert Luthuli

Shi ne dan kasar Afirka ta Kudu na farko da ya samu kyautan a 1960 saboda yadda ya yi yaki da nunawa bakaken fata banbanci a kasar ba tare da tayar da rikici ba. Shine shugaban African National Congress (ANC).

A wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa Farai minitan Habasha, Abiy Ahmed shima ya samu kyautan Nobel a ranar Juma'a 11 ga watan Oktoba saboda sulhu da ya yi da kasar Eritrea da ta dade tana gaba da kasarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel