Babbar magana: Kadan ya rage na kashe kaina bayan na kama saurayina yana zina da mahaifiyarsa - Budurwa

Babbar magana: Kadan ya rage na kashe kaina bayan na kama saurayina yana zina da mahaifiyarsa - Budurwa

- Wata budurwa ta bayyana yadda ta kusa kashe kanta bayan ta ga wani abu da yayi mutukar tada mata hankali

- Budurwar ta bayyana cewa ta iske saurayinta wanda ta shafe shekara biyu tana soyayya da shi yana zina da mahaifiyarsa

- Budurwar ta ce ba ta taba tunanin saurayin nata zai yi mata haka ba

Wata budurwa 'yar shekara 20 a duniya wacce aka boye sunanta, ta bayyana yadda ta kusa kashe kanta bayan ta iske saurayinta dumu-dumu yana zina da mahaifiyarsa wacce ta tsugunna ta haife shi.

Buduruwar dai ta nuna rashin jin dadinta a shafin sada zumunta na zamani, inda ta ce:

"Ina soyayya da saurayina tun ina 'yar shekara 18 a duniya, yanzu shekara ta 20. Saurayina ya bayyana mini cewa babu matsala dan iyayen mu mata sun kwanta a dakin da muke ko da kuwa ina nan.

"Wata rana da yamma, sai na tafi gidan su saurayina na fada masa cewa ina so naje asibiti. Ina shiga dakin da suke sai na tarar da shi yana lalata da mahaifiyarsa wacce ta tsugunna ta haife shi, wallahi na kusa kashe kaina a lokacin da na ga wannan abu.

KU KARANTA: A karshe dai Dangote yayi martani ga gajeren wadan da yake bayyanawa duniya cewa ya fishi kudi

"Ni ba wai shawara nake nema ba, ina so na sanar da duniya cewa samarin Benue 'yan iska ne. Ku boye sunana na, naji kunya sosai."

Fitaccen mai bawa ma'aurata shawara a fannin aure, Joro Olumofin shine ya wallafa wannan labari a shafinsa na Instagram ranar Asabar dinnan da ta gabata.

Saurayin wanda budurwar ta bayyana cewa dan jihar Benue ne tana zargin shi da lalata da mahaifiyarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel