Cutar shawara tana yin dauki dai dai a Bauchi, ta kashe mutuane 22

Cutar shawara tana yin dauki dai dai a Bauchi, ta kashe mutuane 22

Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta jahar Bauchi ta tabbatar da mutuwar wasu mutane guda 6 a jahar a sakamakon kamuwa da suka yi da cutar shawara, watau Yellowe fever a turance, inji rahoton Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito zuwa yanzu adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar cutar shawara sun kai mutum 22 a jahar Bauchi kadai, tun bayan barkewar cutar a gandun dabbobi na Yankari dake karamar hukumar Alkaleri.

KU KARANTA: Yan Najeriya miliyan 15 ne suke fafutukar neman aikin yi a Najeriya – Gwamnati

Haka zalika an samu barkewar cutar a karamar hukumar Tafawa Balewa inda har mutane uku suka mutu. Kisan farko da cutar ta yi shine na wasu daliban kwalejin ilimi na Waka-Biu dake cikin karamar hukumar Biu ta jahar Borno.

Su dai wadannan dalibai sun kai ziyarar bude ido ne zuwa gandun dabbobi na Yankari inda suka kamu da cutar, mutane hudu sun mutu daga cikinsu yayin da aka kwantar da dalibai 12, wadanda suka mutu sun yi korafin ciwon ciki tare da amayar da jini kafin mutuwarsu.

A ranar 5 ga watan Satumba ne gwamnatin jahar Bauchi ta tabbatar da barkewar cutar, kamar yadda shugaban hukumar kiwon lafiya, Dakta Rilwan Mohammed ya bayyana, a jawabinsa yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Litinin, Rilwan yace sun samu mutane 143 da alamun cutar, amma a mutane 24 aka tabbatar da ita.

Daga cikin mutane 24 da gwamnatin ta tabbatar ne aka samu mutane 22 da suka mutu, kuma dukkaninsu yan asalin karamar hukumar Alkaleri ne, haka zalika 10 daga cikin 22 da suka mutu jami’an kula da gandun dabbobin ne a dakin Yankari.

A yanzu haka Rilwan yace sun cimma kashi 79 na allurar riga kafin da suke yi ma jama’a don kariya daga cutar shawarar, amma yace har yanzu akwai mutanen da basa yarda a yi musu wannan allurar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel