A jihar Kano, an saki sunayen yara 47 da aka sace

A jihar Kano, an saki sunayen yara 47 da aka sace

Kungiyar Iyaye da aka sace musu yara sun saki jerin sunayen yara 47 da aka sace musu kuma aka kai kudancin Najeriya.

A ranar Asabar, hukumar yan sandan jihar Kano ta ceto yara tara da aka wasu inyamurai suka sace daga jihar Kano zuwa garin Onitsha a jihar Anambara kuma suka sayar da su.

Hukumar ta gudanar da binciken ne biyo bayan kukan da iyaye suka kai cewa yaransu na bacewa a unguwa.

A ranar Alhamis, shugaban kungiyar iyayen, Tajiri Hotoro, ya ce adadin yaran da aka sace a shekaru hudu da suka gabata a karamar hukumar Nasarawa kadai ya fi 100, Daily Nigerian ta bada rahoto.

Yayinda yake gabatar jerin sunaye da hotunan yaran, Malam Tajiri ya ce akwai iyaye da dama da suka ki rijista da kungiyar.

SHIN KA KARANTA WANNAN? Mafi karancin albashi: Gobe za'ayi zaman karshe tsakanin gwamnati da yan kwadago

Yace: "Akwai iyaye da dama da suka hakura. Wasu ko kudin motan zuwa ganawarmu basu da shi."

"Muna kira ga gwamnati da hukumar su taimaka wajen ceto mana yaranmu. Muna cikin halin takaici"

A shekaru biyu da suka wuce, yan sanda sun damke wasu amma daga baya aka sakesu.

Ga sunayen:

A jihar Kano, an saki sunayen yara 47 da aka sace
A jihar Kano, an saki sunayen yara 47 da aka sace
Asali: Facebook

A jihar Kano, an saki sunayen yara 47 da aka sace
A jihar Kano, an saki sunayen yara 47 da aka sace
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel