Dan marigayi tsohon shugaban kasa a mulkin soja ya mutu

Dan marigayi tsohon shugaban kasa a mulkin soja ya mutu

John Nnanyerem Aguiyi Ironsi, dan marigayi tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Johnson Thomas Aguiyi Ironsi, na biyu ya mutu.

A cewar jaridar Daily Trust, dan Ironsi ya mutu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Oktoba a cibiyar lafiya ta tarayya, Umuahia, jihar Abia, biyo bayan wani rashin lafiya da yayi.

Legit.ng ta tattaro cewa babban jigon ahlin Ironsi kuma tsohon karamin ministan tsaro, Thomas Aguiyi Ironsi, ne ya tabbatar da labarin mutuwar a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba.

An haifi marigayin a ranar 14 ga watan Janairun 1965 sannan ya halarci makaantar kwalejinGwamnati, Umuahia, jihar Abia da kuma kwalejin kimiyya, Zaria, jihar Kaduna, kafin ya tafi kasar Amurka don cigaba da karatunsa.

KU KARANTA KUMA: Ba mutunci: Yadda Aisha Buhari ta yi mana 'tatas' a fadar shugaban kasa - Diyar Mamman Daura

Bayan dawowarsa Najeriya, ya riki mukaman siyasa a matsayin hadimi na musamman ga gwamnonin jihar Abia daban-daban har su biyu.

Ya mutu ya bar matar aure guda yarinya daya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel