Tsotson nonon matan aure na taimakawa wajen gane cutar kansan da wuri - Likita ta shawarci mazajen aure

Tsotson nonon matan aure na taimakawa wajen gane cutar kansan da wuri - Likita ta shawarci mazajen aure

Wata Likita mai suna, Abigail Shona, ta yi kira ga mazajen aure su rika tsotson nonon iyalansu saboda hakan kan taimaka wajen gane yiwuwan cutar kansan nono, hakazalika shayar da yara nono kan kare citar dajin.

Dakta Shona ta bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya hakan ne ranar Litinin a Ilori inda ta ce sabanin abinda wasu ke tunanin, shan nonon matan aure bai hana cutar kansa amma yana taimakawa wajen ganoshi da wuri.

Ta ce shayar da yara nono ne ke kare cutar kansa.

SHIN KA KARANTA WANNAN? Sarkin Kano ya sallameni don na karrama Ganduje - Maji Siddin Sarki

Tace: "Yawancin matan da shayarwa na fuskantar wasu sauye-sauye a jikinsu wanda ke jinkirta dawowan jinin al'ada."

"Hakan na rage girman Estrogen wanda ke taimakawa wajen girman kwayar kansa."

"Abinda tsotson nono da maza ke yi kadai shine yana taimakawa wajen gane cutar kansa da wuri saboda guda-gudan da za'a ji."

"Muna kira ga mata kada su hana mazajensu dadin tsotson nononsu da wasa da shi saboda hakan zai yi musu amfani."

"Dalilin hakan shine duk da shawaran da muke baiwa mata su ria dubawa da kansu domin ganewa, yawancinsu basu yi."

"Amma idan suka bari mazajensu suka yi musu, zai taimaka matuka wajen ganoshi da wuri kuma hakan na da muhimmanci wajen maganceshi."

"Idan an gano cutar kansa da wuri, za'a iya waraka daga shi kafin yayi tsauri."

Ta kare da cewa maza na iya kamuwa da cutan kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel