Fatun Layya: Kungiyar Izala Ta Tara Naira Miliyan 65.8

Fatun Layya: Kungiyar Izala Ta Tara Naira Miliyan 65.8

Layya ta yi albarka: Kungiyar yada da'awar addinin Musulunci, Jama'atu Izalatul Bid'a wa iqaamatus Sunnah watau JIBWIS ta bayyana cewa ta samu milyan 65.8 daga fatun Sallan layyan bana.

Shugaban kungiyar Izala Ash-Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau ya karbi rahoton kwamitin karban sadakar fatun layya. Kwamitin ya karbi fatun dabbobi a sallar layya da ya gabata a duk fadin jihohin Nijeriya, kungiyar ta bayyana.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a jawabin da ta saki a shafin ra'ayi da sada zumuntarta a ranar Lahadi, 14 ga Oktoba, 2019.

KU KARANTA: Idan kuka siya mana jirage masu angulu, Boko Haram za ta zama tarihi - Hukumar Soji

Jawabin yace:

"A shekarar bana (1440/2019) kungiyar Izala ta samu jimillar kudi Naira Miliyon sittin da shida, da dubu dari takwas da tamanin da hudu da Naira dari biyar da goma sha biyu da kobo saba'in da biyu (N66, 884, 512. 72.) daga sadakan fatun layyan a fadin Nijeriya."

"Sheikh Bala Lau ya jinjinawa al-umman musulmai da suka bada taimakon fatu daga ko ina a Nijeriya. Yace kamar yanda jama'a suka sani yanzu haka kungiyar na gina katafaren masallaci a cibiyar ta dake Abuja wanda kuma kai tsaye wannan kudi da aka samu zasu tafiyar da shi akan wannan aikin."

"Ko a shekarun da suka gabata, kungiyar ta kaddamar da katafaren gidan masaukin baki a birnin tarayya Abuja inda ta bayyana cewa da taimakon da jama'a suka bayar na fatun layya aka gina. Ko a bara ma kungiyar ta sanar da asibiti da take ginawa da kudin na fatun layya."

"A bana jihar Kaduna ita tayi na daya wajen tara fatun layya da yawan su yakai dubu (19,913) tare da taimakon kudi Wanda jimillar su yakai adadin dubu (N8,128,840)."

"Jihar Sokoto ita tayi na biyu wajen tara fatun layya guda dubu (13,754) tare da gudunmawar kudi Wanda jimillar kudin fatu da na taimako yakai adadin (N7,315,360)."

"Jihar Zamfara ita tayi na uku wajen tara fatun layya guda dubu (13,804) tare da gudunmawar kudi Wanda jimillar kudin fatu da na taimako yakai adadin (N6,840,610)."

Asali: Legit.ng

Online view pixel