Gaskiyar lamari: Yar Mamman Daura ce ta dauki bidiyon Aisha Buhari tana fada

Gaskiyar lamari: Yar Mamman Daura ce ta dauki bidiyon Aisha Buhari tana fada

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa sabon Baraka ta kunno kai a fadar Shugaban kasa bayan anyi ta yada jita-jita game da zargin Karin auren Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A lokacin da ake ganiyar yada jita-jitan Karin auren Shugaban kasar, wani bidiyo ya yi ta yawo a shafukan zumunta, inda aka nuno uwargidar Shugaban kasar, Aisha Buhari tana ta tayar da jijiyoyin wuya kan wani batu.

Mutane da dama sun ta alakanta bidiyon da cewa Aisha ce ta dawo daga kasar Ingila tana fada cewa an rufe mata kofa.

Sai dai uwargidar Shugaban kasar bayan dawowarta daga Ingila ta tabbatar da cewar ita ce a cikin bidiyon amma ta ce tsohon bidiyo ne.

Harma Aisha Buhari ta jaddada cewa Fatima 'yar gidan Mamman Daura ce ta nadi bidiyon da ake tafka mahawara a kai.

Ta ce: "Jami'an tsaro na suna wurin amma sun kasa yin komai domin 'yar gidan Mamman-Daura Fatima ce ta dauki bidiyon kuma har yau ni da su mun kasa yin komai kan lamarin."

Haka zalika a hirar da aka yi a harshen Hausa ta nanata cewa Fatima ce ta dauki bidiyon, har tana yi ma ta dariya kuma ita ce ta rufe ma ta kofar dakin ajiyar kayayyaki.

Da aka tuntubi Fatima Mamman Daura, ba ta karyata daukar bidiyon ba, sai dai ta ce ta dauki bidiyon ne domin ta nuna wa iyayenta da jami'an tsaro a matsayin shaida ko da wani abu ka biyo baya.

Fatima ta bayyana cewa tun bayan hawan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shugaban ya bai wa mahaifinta (Mamman Daura) wurin zama a cikin fadar shugaban kasa wanda ake kira ''Glass House.''

Ta ce a lokacin da Yusuf Buhari ya samu hatsari a kwanakin baya, Shugaba Buhari ya bukaci Mamman-Daura da ya koma wani gida da ake kira ''House No. 8'', wato gida mai lamba 8 domin a yi jinyar Yusuf a gidan da Mamman Daura da iyalensa suke zaune domin wurin ya fi kusa da inda Aisha Buhari ta ke.

Fatima ta bayyana cewa ko da hakan ya faru iyayenta ba su kasar, sai dai mahaifinta ya ba ta umarnin ita da ýar uwarta, cewa su kwashe kayansu daga gidan a ranar wata Asabar.

Ta bayyana cewa suna cikin kwashe kayansu ne sai ta jiyo hayaniya, domin ita tana can cikin uwar daki 'yar uwarta kuma tana dakin waje wanda ya fi kusa da kofar shiga gidan.

KU KARANTA KUMA: Sanusi ya karyata sallamar basarake saboda yiwa Ganduje maraba

Ta ce kofar da ke waje an saka mukulli an rufe domin yawanci idan suna ciki su kan rufe ta.

Ta bayyana cewa ko da Aisha ta zo ta ga kofar a rufe, ''ta yi amfani da kujerar karfe wajen balle kofar.''

A cewar Fatima, wannan dalili ne ya sa ta dauko waya domin yin bidiyo don ya zama shaida.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel