Furuci 10 da bai kamata miji ya yi wa matarsa ba
Cimma burin kauna ko kawar da sha'awa da debe wa juna kewa ba su kadai bane ababen da ke wanzar da zaman lafiya a tsakanin ma'aurata, babu shakka akwai bukatar mutunta juna a tsakanin miji da mata. Kuma akwai bukatar kowace matar aure ta girmama mijinta ta yadda shi ma zai ba ta nata girman kwatancin yadda ta girmama shi.
Koda ya ke Hausawa na cewa zo mu zauna daidai ya ke da zo mu saba, kowane ma'aurata na muradin zaman lafiya mai dore wa a tsakanin su da juna.
Ba ya ga kasancewa aboki ga matarka, ana kuma son miji ya kasance mai kyautata mu'amalarsa da ita ta fuskar magana mai dadi, debe kewa da kuma sanya mata farin ciki gami da nutsuwa.
Miji ya kasance mai taimakon matarsa yayin da ta shiga tsanani, tare da debe mata kewa a yayin da ta ke cikin kadaici ta hanyar janta a jika. Haka kuma kowace mace na bukatar yabo daga wurin mai gidanta a duk sa'ilin da ta yi yunkurin kyautata masa.
Magabatan kwarai sun ce gishirin zaman aure shi ne hakuri, a yayi da wasunsu kuma ke jaddada muhimmancin rikon amana da gaskiya.
KARANTA KUMA: Dattawan Kano sun bayyana damuwa kan yaran da aka ceto daga hannun masu safarar mutane a jihar Anambra
A wani rahoto da muka kalato daga jaridar The Nation mun samu cewa, akwai wasu nau'ikan kalamai da bai kamata miji ya rinka yi wa matarsa ba domin kuwa hakan yana sanya radadi a zuciyarsu.
Nau'ikan furuci masu fito wa daga harsunan mazaje cikin fushi wadanda ke harzuka matan auren sun hadar:
'ya rage naki'
'ki 'karata'
'kin fiya lalaci'
'fita ki bani wuri ko kuma 'bace min daga nan'
'aikin kenan ko kuma kullum haka kike'
'ki bari ba yanzu ba, sai zuwa gaba'
'laifin ki ne ai'
'ban sani ba'
'ki tafi gidanku ai miki'
'kina samun irin haka a gidanku'
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng