Da duminsa: An kai hari gidan Adams Oshiomole

Da duminsa: An kai hari gidan Adams Oshiomole

An samu tashin hankali a jihar Edo ranar Lahadi sakamakon rahoton cewa an kai hari gidan shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, Adams Oshiomhole.

Wasu fusatattun matasa sun dira gidan Adams Oshiomole inda suke ihun 'Oshiomole barawa Oshiomole barawo' amma yan sanda sun fitittikesu.

Mai magana da yawun Oshiomole, Mista Simon Ebegbulem, ya bayyana cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ne ya tura yan daba su ci mutucinsa.

Ya ce wannan hari da suka kai na daya daga cikin shawarin da aka yanke a taron majalisar zantarwan jihar na cin mutuncin duk wadanda basu goyon bayan tazarcen gwamnan.

Kwamishanan yan sandan jihar, Danmallam Abubakar, ya musanta cewa hari aka kaiwa Oshiomole, ya ce wasu ne kawai suke gudanar da zanga-zanga kuma an tarwatsa su.

Yace: "Karya ne, babu wani hari. Babu abinda ya faru a unguwar da Oshiomole ke zaune."

KU KARANTA: Bayan biyan kudin fansan N5m, an sako mutane 8 da aka sace a Abuja

A bangaren gwamnati, mai magana da yawun gwamnan jihar, Mista Crusoe Osagie, ya ce zargin da ake yiwa gwamnan sharri ne.

A cewarsa: "Gwamnatin jihar Edo ta ce ba tada wani masaniya kan wani harin da aka kai gidan tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole."

"Bamu da masaniya akan harin. Mun tuntubi jami'an yan sanda kuma sun tabbatar da cewa basu da wani labari kan hakan."

Wannan ya biyo bayan dambarwan siyasan da ke gudana tsakanin Adams Oshiomole da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel