Daga samun labarin mutuwan matarsa, wani fasinja ya yanke jiki ya fadi a filin jirgin Legas

Daga samun labarin mutuwan matarsa, wani fasinja ya yanke jiki ya fadi a filin jirgin Legas

A ranar Asabar, wani fasinjar jirgin sama mai suna, Jude Oladapo, ya yanke jiki ya mutu yayinda yake shirin shiga jirgi a babban filin jirgin saman kasa da kasa na Murtala Muhammed International Airport (MMIA), Lagos.

Kakakin ofishin hukumar yan sandan na filin jirgin saman, DSP Joseph Alabi, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai ranar Lahadi a Legas.

DSP Joseph Alabi ya ce fasinjan wanda ya nufi shiga jirgin Air France ya yanke jiki ya fadi ne bayan samun labarin mutuwar matarsa.

A cewarsa, wannan abu ya faru misalin karfe 5:30 na yamma kuma likitan asibitin filin jirgin saman MMIA Clinix, Dakta Ajayi Olamide, ya tabbatar da mutuwarsa.

Alabi ya ce tuni an ajiye gawarsa a dakin ajiye gawawwakin asibitin Air Force.

KU KARANTA: Na tafi Ingila jinya ne - Aisha Buhari

A wani labarin daban, An sako mutane takwas cikin goma da aka sace ranar Litinin da ya gabata a unguwar Pegi, karamar hukumar Kuje a birnin tarayya Abuja.

Bayan roko da lallashi, an samu labarin cewa an sako mutanen ne sun yi aman milyan biyar na fansa. The Naton ta bada rahoto.

A cewar majiya, masu garkuwa da mutanen sun ci mutuncin mutanen kan gazawar iyalansu wajen biyan kudin fansan da suka bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel