Zaben Kogi: Hotunan Wada yana sharbar barci a wurin taro ya karade shafukan sada zumunta

Zaben Kogi: Hotunan Wada yana sharbar barci a wurin taro ya karade shafukan sada zumunta

Jaridar Vanguard ta wallafa wasu hotunan Injiniya Musa Wada yana sharbar barci a wurin wani taro.

Wada ne dan takarar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da za a gudanar a jihar Kogi a ranar 16 ga watan Nuwamban 2019.

A cewar rahoton, hoton ya janyo cece-kuce tsakanin wasu mambobin na jam'iyyar PDP.

Rahoton ya ce an jiyo wani jigo a PDP da ba a bayyana sunansa yana cewa, "Wannan abin kunya ne. Dan takarar gwamnan mu da mataimakinsa duk suna barci a wurin taro, wannan ba alama ce mai kyau ba kuma ba za mu amince da hakan ba."

Hotunan dan takarar gwamnan PDP yana sharbar baci a wurin taro ya janyo cece-kuce
Hotunan Wada yana sharbar barci a wurin taro
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zamfara: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 100 yayin da suka yi yunkurin kai hari gonar tsohon gwamnan jihar

Da ya ke tsokaci kan hoton, wani jigo a jam'iyyar APC da Vanguard ta zanta da shi ya ce: "Ta yaya shi da mataimakinsa za su rika barci a taro na awa biyu? Ya kamata a ce suna cikin koshin lafiya kafin suyi tunanin za su iya karbe mulki daga hannun Gwamna Yahaya Bello da ke jan ragamar mulkin jihar da kyau duk da karancin kudi."

Wada, kanin tsohon gwamnan jihar, Kyaftin Idris Wada (ritaya) zai fafata da dan takarar jam'iyyar APC kuma gwamna mai ci a yanzu Yahaya Bello a zaben da za ayi a watan Nuwamba.

A halin yanzu, kungiyar kabilar Ebira na jihar tayi kira ga al'ummar jihar su mara wa Gwamna Bello baya a zaben.

Shugaban kungiyar, Dr Adeiza Musa Abdulrahman ne ya aikewa manema labarai sanarwar a ranar Laraba 9 ga watan Oktoba inda ya ce dukkan masu son cigaba sunyi na'am da irin kamun ludayin Gwamna Bello.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel